1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Najeriya ta dauki sabon salo

August 9, 2018

A wani abin da ake yi wa kallon dorawa a cikin rikicin zabukan shekara ta 2019, hukumar EFCC ta rufe daukacin asusun jihohin Benue da Akwa Ibom da ake ganin suna da tasiri ga adawa.

https://p.dw.com/p/32u9e
Nigeria Plakate und Aufkleber gegen Korruption
Hoto: DW/K. Gänsler

Sama da Naira miliyan dubu 20 ne dai Abujar ta ce ta bayar da suna na tallafi ga biyan albashin ma'aikata a jihar Benue da ke fama da rigingimun tsaro. To sai dai kuma har ya zuwa yanzun ma'aikatan jihar na bin bashin albashin da ya kai na kusan watanni 12 cikin jihar. Babbar hujjar kuma da a cewar hukumar EFCC mai yaki da halasta haramun ya sanya ta rufe asusun gwamnatoci na Benue da ake zargin gwamnan jihar Samuel Ortom da karkatar da kudade dama yar uwarta ta Akwa Ibom da ita ma tai nisa a cikin rikicin albashin. Wata sanarwar EFCC dai ta ce babu ko kobo da zai fita daga asusun jihohin guda biyu har sai an kamalla bincike bisa yadda kudaden sukai batan dabo da sunan albashi da ragowar aiki na kasa. To sai dai kuma matakin da yazo daidai lokacin da fagen siyasar Tarrayar Najeriyar ke kara dumi, tuni ya fara jawo kace nace a tsakani na 'yan kasar da ke masa kallon da biyu.

 


A yayin da tuni gwamnan jihar ta Benue yai nisa da  tsintsiyar  APC, can a Akwa Ibom dai komawar tsohon gwamnan jihar Godswill Akpabnio da ke rikici da mutumin da ya mikawa mulki zuwa APC na da ruwa da tsaki da sabon matakin. Ita kanta kungiyar  gwamnonin jihohin kasar ta ce an saba ka'ida ga batu na rufe asusun, da ke iya shafar daukacin aiyyuka na gwamnati musamman ma a jihar Benue da ke kokarin fitowa a cikin matsalar tsaro.To sai dai kuma in har ta saba a tunanin gwamnonin, ga su kansu ma'aikatan da EFCC ke kokarin burgewa, sunce ba su yarda da sabo na matakin da a cewarsu zai kai ga kara bata lamarin maimakon gyara a kokari na neman mafitar. Komrade Kabir Nasir dai na zaman kakakin hadaddiyar kungiyar kodagon UAD da kuma ya ce ya zama wajibi ga gwamnatin na sakin mara ga jihohin guda biyu da nufin hana tsaikon lamura a cikinsu. Abun jira a gani dai na zaman yadda za ta kaya tsakanin masu takama da hukuncin da ma 'yan tawayen da ke kara nuna alamun bijirewa.

Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba