1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Farfado da shirin afuwa a Niger Delta

Gazali Abdou TasawaMay 29, 2016

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da shirin sake farfado da matakin yin afuwa ga tsagerun Niger Delta a wani mataki na neman kawo karshen hare-haren da suke kaiwa kan cibiyoyin man fetur na kasar

https://p.dw.com/p/1Iwi7
Nigeria Präsident Amtseinführung von Muhammadu Buhari
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da shirin sake farfado da matakin yin afuwa ga tsagerun Niger Delta a wani mataki na neman kawo karshen hare-haren da suke kaiwa kan cibiyoyin man fetur na kasar, da kuma ke haifar da koma baya ga aikin hakar man.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a cikin wani jawabi da ya gabatar a wannan Lahadi albarkacin zagayowar ranar cikon shekara daya da hawansa mulki.

A baya dai Shugaba Buhari ya sanar da takaice shirin yin afuwar dama dakatar da shi a karshen shekara ta 2018 kafin a halin yanzu ya sanar da sake farfado da shi a bisa a cewarsa dalillai na neman samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin mai arzikin man fetur.

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa hare-haren baya-bayan nan da tsagerun suka kaddamar kan cibiyoyin aikin man, ba za su hana masu ba neman yin sulhu. Shirin yin afuwa da Najeriyar ta soma a shekara ta 2009 ya tanadi biyan albashi ga tsaffin mayakan yankin dubu 30 da kuma samar masu da aikin yi.