1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

HRW: Mun yi farin ciki da rahoton kisan EndSars

Uwais Abubakar Idris MNA
November 19, 2021

Human Rights Watch ta ce gaskiya ta yi halinta kan zargin mutanen da jami'an tsaron Najeriya suka kashe a lokacin zanga-zangar EndSars, biyo bayan rahoton kwamitin da gwamnati ta kafa da ya nuna cewa lallai an yi kisan.

https://p.dw.com/p/43GI7
Nigeria Lagos | EndSars Demonstration
Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Rahoton na kungiyar kare hakin jama'ar ta Human Rights Watch da ya bayyana cewa abin da ya faru ya nuna a fili cewa karya dai fure take ba ta 'ya'ya, domin kwamitin da gwamnatin Najeriya ta kafa a kan kashe-kashen da aka yi na fararen hula a lokacin zanga-zangar EndSars da kansa ne ya karyata dukkanin dagewar da gwamnatin Najeriya ta yi a kan wannan batu da ake ci gaba da yamadidi a kansa.

Karin bayani: Rahoton ENDSARS ya bar baya da kura

Human Rights Watch ta ce rahoton da gwamnatin ta fitar mai shafuka 309 ya jaddada matsayinta ne, domin tun da dadewa ta bayyana cewa lallai an yi kisa na mutanen da ba su rike da wani makami a lokacin zanga-zangar a ranar 20 ga watan Oktoban 2020. Anietie Ewang ita ce jami'a mai bicike a kungiyar.

"Muna nuna farin cikinmu a game da wannan rahoto wanda ya tabbatar da binciken da tun da farko muka yi, amma abin da ya faru alamu ne na nasara da ya nuna lallai hukumomi in an ba su dama za su iya gudanar da aiki, kuma za su iya samar da rahoton da ya tsage gaskiya. Saboda haka muna bai wa hukumomin kwarin gwiwa su yi abin da ya dace, a aiwatar da shawarwarin da aka bayar ta yadda za a yi gaskiya a bar kawar da kai wajen hukunta masu laifi tare da kare hakokin jama'a."

'Yan sandan Najeriya sun ja daga a Lekki Tollgate da ke Legas a ranar cika shekara guda da zanga-zangar EndSars ranar 20 ga watan Oktoban 2021
'Yan sandan Najeriya sun ja daga a Lekki Tollgate da ke Legas a ranar cika shekara guda da zanga-zangar EndSars ranar 20 ga watan Oktoban 2021Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images

Dama dai a kan ce shure-shure baya hana mutuwa bisa ga yadda gwamnatin Najeriya ta dage da babu abin da ya faru, amma binciken da ita da kanta ta kafa kwamiti ya bankado wannan abu har da shaidun lokaci da wadanda aka kashe a yanayi na allura ta tono garma.

Karin bayani: Najeriya na biyan diyyar asarar EndSars

Ko da yake daga kungiyoyin kare hakin jama'a na Najeriyar da ma kasashen waje murna har ciki a kan gano gaskiyar lamari, amma ga Barrister Mainasara Umar, masani a kan tsarin mulkin Najeriyar ya ce "akwai fa sauran aiki a gaba bisa ga fahimtar kwamitin da gwamnatin jiha ta kafa a kan hukumar 'yan sanda da yake ba ta da iko a kanta."

Tuni dai gwamnatin tarayyar Najeriyar ta ce za ta sa ido don ganin abin da gwamnatin jihar Legas za ta yi da sakamakon rahoton don hukunta wadanda ake zargi da aikata ba dai dai ba, kama daga 'yan sanda da sojojin da ba ta da iko a kansu.