1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani cikin jam'iyyar APC a Najeriya

June 1, 2022

A yayin da jam'iyyar APC ke kara kusantar zaben fidda gwani a cikin makon gobe, kan jiga-jigan 'ya'yanta na kara rabuwa tsakanin masu tunanin samar da dan takarar jam'iyyar ta dabarar sulhu da masu tunanin gwada karfi.

https://p.dw.com/p/4C9de
Muhammadu Buhari I Shugaban Kasa I Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, na shirin tsayar da magajinsa a APCHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Sau biyu ne dai cikin sa'o'i 24 gwamnonin jam'iyyar 22 suka gudanar da taron gaggawa, sau biyun kuma ana tashi baram-baram sakamakon gaza cimma daidaito kan tsarin da ya da ce masu tsintsiyar su dauka a babban zaben jam'iyyar a makon da ke tafe. Cikin tsakiyar rikicin dai, tials a kai ga fitar da dan takarar da APC ke fatan ya jagoranci jam'iyyar a zaben Najeriyar na 2023. Wata ganawa a tsakanin shugaban kasar da gwamnonin jam'iyyar dai ce ta kai ga ballo rikici, bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya shaidawa gwamnonin burinsa na fitar da dan takara guda da daukacin kasar ka iya amince masa. Duk da cewar dai shugaban bai fito fili ya ayyana suna da kila ma yanayi na magajin nasa ba, Buharin dai ya bude kofar da magoya bayansa ke fadin sulhu na zaman kan gaba cikin zabin nasa.

Najeriya | PDP I Takara I Shugaban Kasa
Atiku Abubakar ne zai yi wa jam'iyyar adawa ta PDP takarar shugaban kasa a NajeriyaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

A baya dai shugaban yace yana da zabi na magajin da ba zai ambaci sunansa ba, domin ba shi kariya daga kurayen jam'iyyar. Koma ya take shirin kayawa a tsakanin gwamnonin, batun na sulhu dai a tunanin wasu 'ya'yan jam'iyyar na da babban burin tilasta dan takarar na Buhari a kan sauran masu takarar. Duk da cewar dai APC na iya kai wa ga samar da mai karfi sai Allah a cikin babban taron, akwai kuma tsoron tsinke daurin tsintsiyar da kila ma watsewarta sakamakon gwada kwanjin. Abun kuma da a cewar Abubakar Mai Kudi da ke zaman jigon jam'iyyar, yasa ake da bukatar kallon tsaf tare da kaucewa shiga rudani a takarar. Fitowar da Atiku Abubakar domin jagorantar 'yan lema a zaben na badi ne dai, daga dukkan alamu ke yin gizo ga masu tsintsiyar da ke tsoron fuskantar zabe da dan takara mai da raunin gaske. To sai dai kuma ja da Buharin a cikin fatan samar da dan takara mafi farin jini cikin APC dai, a tunanin Faruk BB Faruk da ke sharhi kan siyasa ta kasar na kama da daukar dala a bangaren gwamnonin.
 LINK: