1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jan hankalin matasa su guji shiga bangar siyasa

Uwais Abubakar Idris MNA
December 4, 2018

Kungiyar matasan Kiristocin a Najeriya na daukar matakai na jan hankalin matasa su guji shiga rigingimun siyasa a daidai lokacin da yakin neman zabe ke kankama.

https://p.dw.com/p/39Soq
Nigeria - Jugenddemonstration "not too young" in Abuja
Hoto: Uwais Abubakar Idris

Kauce wa kokari na amfani da matasa domin su tayar da hankali a lokacin yakin neman zabe da ma zaben kansa ya sanya kungiyar Kiristocin Najeriya gudanar da gangami na musamman domin fadakar da matasan hatsarin da ke tattare da hakan. Matakin da ya sanya jawo su a jika da ma yi masu kashedin bari a yi amfani da su.

A taron da wakilan matasan suka gudanar a birnin Abuja, fadar gwamnatin Najeriya, daya a cikin jerin abubuwan da suka tsara yi don samun zaman lafiya. Shin akwai abin da suka hango ne ya sanya su yin wannan? Pastor Bitrus Dan Giwa jami'i ne daga cibiyar wanzar da zaman lafiya ta mabiya addinai da ke Kaduna.

Gangamin siyasa a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya
Gangamin siyasa a jihar Zamfara da ke arewacin NajeriyaHoto: DW/Y.I. Jargaba

"Mun lura cewa har yanzu 'yan siyasa suna amfani da matasa a matsayin 'yan bangar siyasa domin a kawo rashin zaman lafiya.Muna wayar musu da kai da ka da su yarda wani dan siyasa ya yaudare su da kudi. Idan abin na da kyau to 'yan siyasar su sanya 'ya'yansu a cikin 'yan bangar mana."

Kama daga jihar Filato zuwa Kaduna da Zamfara da ma yankin Niger Delta tashe-tashen hankula sun kasance abubuwa da ke daga hankali sosai, ganin an daga kugen siyasa tuni an fara tarba-tarba na tabbatar da kawar da duk wani rikici musamman saboda zaben. Barrister Samuel Kwamkur na daya daga cikin shugabannin kungiyar Kiristocin Najeriya.

"Masu iya magana suka ce zama lafiya ya fi zama dan sarki. Ya kamata duk dan Najeriya ya zama mai kyaunar zaman lafiya. Yanzu da aka fara yakin neman zabe muna son mu tabbatar cewa ba a yi amfani da matasa a ta da hankali ko wani rikici na bau gaira babu dalili ba."

Solomon Dalung, ministan matasa da wasanni na Najeriya
Solomon Dalung, ministan matasa da wasanni na NajeriyaHoto: DW/U. A. Idris

Ita kanta gwamnati na bayyana daukar matakai na amfani da wasanni domin kara sanya kaunar juna da hadin kai a tsakanin matasa na Najeriya, abin da Mr Solomon Dalung ministan matasa da wasanni ya bayyana amfani da gasar kakar wasanni na kasa ta Najeriya.

"Tun a shekarar 1973 aka fara wasannin. Wanda za mu yi na cikon 19 matasa ne mafi yawan wadanda ke cikin wasannin. Idan suka shaku da juna tun yanzu, za su watsi da duk wani bambance-bambance. Za su girmama juna za su yi watsi da duk wani bambanci na kabila."

To sai dai an dade ana nuna 'yar yatsa ga gwamnati a kan rashin hukunta wadanda suka aikata ba daidai ba a harka ta da fitina da rigingimu na siyasa, abin da Pastor Bitrus Dan Giwa ya ce ya kamata su nuna misali.