1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matakan kakkabe 'yan bindiga a Katsina

May 20, 2020

Sakamakon umarnin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar na kakkabe 'yan bindiga a jihar Katsina, ita ma rundunar 'yan sandan kasar ta kaddamar da yaki da 'yan bindigar a jihar.

https://p.dw.com/p/3cYNq
Symbolbild | Nigeria | SWAT
Kokarin kawo karshen hare-haren 'yan bindiga a KatsinaHoto: AFP/Y. Chiba

Rundunar 'yan sanda kasar ta ce wannan karan ta yi shirin da ba ta taba yi ba na murkushe 'yan ta'addan, inda aka samar wa jami'an runduna ta musamman da ke yaki da 'yan bindigar wato SARS isassun kayan aiki. Sai dai a na ta bangaren gwamnatin jihar Zamfara ta ce kamata ya yi gwamnatin tarayya ta yi shirin yakar 'yan bindigar na bai daya, saboda yanzu haka 'yan sun fara afkawa yankunan jihar. 

Tun bayan da gwamnatin tarayya ta dauki aniyar kakkabe 'yan bindigar a jihar Katsina, al'umma ke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu. Hare-haren 'yan bindigar dai ya janyo asarar dimbin rayuka da dukiyoyin al'umma a jahohin Arewa maso Yammacin Najeriyar, abin da ke sanya tsoro da fargaba ga mazauna jihohin da abin ya yi kamari da ma wadanda ke makwabtaka da su.