1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Doka da Shari'a

Najeriya: Kara kan rijiyar mai ta Malabu

Gazali Abdou Tasawa
December 21, 2016

Hukumar EFCC a Najeriya ta shigar da karar wasu fitattun ‘yan kasar bisa zargin karkatar da dala milyan 1.1 na kudin sayar da rijiyar mai ta Malabu

https://p.dw.com/p/2UglE
Öl Industrie Afrika Arbeiter auf einer Öl Plattform in Nigeria
Hoto: picture-alliance/dpa/dpaweb

Bayan kwashe dogon lokaci ana jan kafa a kan batun badakalar cin hanci da rashawa a kan sayar da rijiyar mai ta 245 da aka fi sani da Malabu, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa ta EFCC ta shigar da karar wasu fitattun ‘yan kasar bisa zargin karkatar da dala milyan 1.1 na kudin, abin da ya sanya maida martani da duba tasirin hakan ga yaki da cin hanci da rashawa. 


Shigar da wannan kara na zama muhimmin mataki da ke cike da tarihi a wannan abin kunya da ya shafi sayar da rijiyar man ta Malabu da shekaru da dama gwamnatocin da suka gabata suka yi biris da lamarin, domin ko da ambato wadanda suka aikata laifin ma ya gaggara balle a kai ga batun sa ran hukunta su. Barista Buhari Yusuf lauya ne mai zaman kansa a Abuja ya bayyana tasirin daukar matakin ga yaki da cin hanci da rashawa:

"Ni dama ban taba fidda zato a kan za a samu mulki irin na yau ba wanda zai zo ya yi bincike a kan irin abubuwan da aka yi na almundahana da kudin kasa. Wadanda suka taimaka wa 'yan Najeriyar da suka yi wannan badakala da cuta, yawanci a kasashensu an hukunta su"

Nigeria Öl im Niger Delta Pipeline in Obrikom
Hoto: AP

Kama hanyar kawo karshen yanayi na 'ya'yan Bowa da Mowa a harakar yakar cin hanci da rashawa a irin wannan badakalar da ta hada da manyan kamfanonin mai irin na Shell da Eni dai, abu ne da ke zama kama hanyar komawa yanayi na ba sani ba sabo, na kowa ya yi a yi mashi a cewar Magaji Da’u Aliyu memba a kwamitin majalisar wakilai da ke gudanar da bicike a kan lamarin na mai yana mai bayyana cewa:


"Dama can ba a bin doka da oda ne, son zuciya aka yi. Dan haka yanzu ba na tsammanin Shugaba Buhari zai sake irin wancan son zuciya da aka yi. Kuma kasancewa muna neman kudi, to wannan wurin zai kawo ma Najeriya wadatattun kudi"


Amma ga Mallam Bashir Baba mai sharhi a kan al’amuran yau da kullum a Najeriya, ko da yake wasu na yabawa amma yana ganin akwai sauran aiki:

Nigeria Niger Delta Ölverschmutzung Öl
Hoto: Getty Images/C. Hondros


"Yanzu muna da sabuwar gwamnati wacce ke ikrarin cin hanci da rashawa, amma duk da haka ina mai tabbatar maka da cewa 'yan nasarar da za a samu, ba za ta kai ta kawo ba daga karshe. Dan haka a ganina abin da ya kamata gwamnati ta duba shi ne maganar harajin dan kasa domin yana da muhimmanci. Saboda halin da ake ciki yanzu, inda ana biya haraji to da Najeriya da 'yan Najeriya sun ga sauyi"


Rijiyar man ta Malabu da ake ta kace-nace a kanta dai bayanai na nuna cewa ita ce wacce tafi arzikin albarakar mai a Afrika domin bisa kiyasi ta na da kimanin gangar mai milyan tara a cikinta. Ga wadanda ke ikirarin su ke da rijiyar man Malabu da aka kwace da karfin mulki a zamanin gwamnatin da ta gabata tare da karkatar da kudinsu, na cike da fatan ganin bayan an hukunta masu laifi an nuna adalci wajen mayar wa wadanda aka gano bisa gaskiya su ne ke da malakar rijiyar ta Malabu don kawo karshen hasarar da Najeriya ke ci gaba da tafkawa.