1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kokarin yaki da cin hanci a majalisa

Ubale MusaAugust 11, 2016

Bayan share tsawon lokaci ana yan kallo, gwamnatin Tarrayar Najeriya ta ce za ta binciki badakalar cusa kudi cikin kasafin kudin da ke tada hankali cikin kasar a yanzu.

https://p.dw.com/p/1Jglq
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Ofishin majalisar dokokin Tarayyar NajeriyaHoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Tuni dai badakalar ta kai ga tada hankula cikin majalisar wakilan kasar dama a wajenta, inda babu zato ba kuma tsammani wani rikicin cikin gida ya rikide ya zuwa annoba babba ta siyasa sakamkon zargin aringizon kudi dama yin cushe a cikin kasafin kudin kasar na wannan shekara. Kuma tuni tsoffin abokai suka koma fara tona asirin juna cikin badakalar da ta dauki hankalin gwamnatin kasar a halin yanzu. Mahukuntan na Abuja dai sun ce suna da niyya ta binciken daukacin kasafin da ma ragowar sa na baya da nufin ganin zaluncin da ke akwai a cikinsa.

Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Ministan shari'ar kasar Abubakar Malami dai ya ce Abujar bata da niyyar kyale duk wani zaluncin da aka kai ga tafkawa da sunan kasafin ko dai a bana ko kuma a shekarun can baya. Suma kungiyoyin fararan hula da ke kallon rikicin a matsayin mai tada hankali, sun share lokaci su na ganawa da shugaban majalisar Yakubu Dogara domin jin daga bakinsa game da badakalar da ake zargin 'yan majalisar da tafkawa.

An dai dauki lokaci ana zargin 'yan majalisar da maida hankali ga kawunansu maimakon biyan bukatun talakawan da suka kai ga dora su a kan mulki, zargin kuma da ke kara tabbatar da sabon rikicin da ya kalli cusa kudade da nufin amfanin kai. Abin jira a gani dai na zaman makomar rikicin da ke dada kamari sannan kuma ke fitar da halin kowa a cikin rana.