1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Korafi kan tabarbarewar harkar shirya zabe

Uwais Abubakar Idris MNA
March 13, 2019

Kungiyoyin farar hula da masu fafutukar kare dimukuradiyya a Najeriya sunyi zanga-zanga a Abuja a kan abi da suka ce tabarbarewar harkar shirya zabe a kasar.

https://p.dw.com/p/3ExHA
Nigeria Regionalwahlen 2019
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Gamaiyyar kungiyoyin farar hula da masu fafutukar kare dimukurdiyya a Najeriya guda 13 sun gudanar zanga-zangar lumana a Abuja, inda suka yi tattaki zuwa hukumar zaben kasar wato INEC don koken abin da suka kira tabarbarewar harkar shirya zabe a Najeriyar

'Ya'yan kungiyoyin masu fafutuar kare dimukuradiyya a karkashin kungiyar ceto dimukuradiyya ta Najeriyar sun rinka rera takensu a gaban hukumar zaben ta Najeriya, inda suka bayyana bacin ransu a kan koma bayan tsarin dimukuradiyya musamman haraar shirya zaben gwamnoni a kasar. Domin shekaru 20 bayan sake kafa mulkin dimukuradiyya a kasar an shiga tsari ne na ci-gaban mai ginan rijiya a kasar. Mallam Mohammed Aminu na cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangar a karkashin kungiyar Save Nigeria.

To sai dai ga Mallam Tijjani Abdulmuminu na kungiyar matasan Najeriya da suka shiga gangamin na mai bayyana cewa su a ganinsu zabubbukan da aka gudanar baya-bayan nan ba a yi adalci an kuma son zuciya a ciki.

Farfesa Mahmood Yakubu shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta INEC
Farfesa Mahmood Yakubu shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta INECHoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Wakilin hukumar zabe dai ya fito inda ya tarbi masu zanga-zangara tare da basu tabbacin za a dauki mataki na tabbatar da adalci a zabubbukan da za a sake yi wadanda aka tsayar da ranar 23 ga watan nan na Maris a jihohin guda shida da suka hada da Kano, Adamawa, Sakkwato, Filato, Bauchi da Benue.

Mr Kelechi Maduneme shi ne jami'in hukumar zabe da ya tarbi masu zanga-zangar.

"Korafe-korafen da kuka kawo a rubuce zan karbe su, ina ba ku tabbacin za a duba su. Amma ku sani za a maimaita zabubbuka a dukkanin jihohin nan shida, kuma za a sanar da wadanda suka ci zabe bisa wadanda suka samu nasara, hukumar ba za ta yi wani abu da ya saba wa hurumin da jama'a suke da shi ba."

To sai dai ga Comrade Isa Tijjani mai sharhi a kan al'amuran yau da kullum na mai bayyana cewa ya kamata a yi hankali da abubuwan da ke faruwa.

Ta kaya ko ba ta kaya ba, 'yan Najeriya na sa ido a kan abin da zai faru a ranar 23 ga watan Maris inda za a maimaita zabubbukan gwamnonin a jihohin guda shida.