1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya samu nasara a kotu

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 11, 2019

A Najeriya, kotun sauraron korafe-korafen zabe, ta yi watsi da karar da dan takarar shugabancin kasar a karkashin babbar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ya shigar gabanta.

https://p.dw.com/p/3PQrZ
Muhammadu Buhari und Atiku Abubakar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buharida dan takarar jam'iyyar adawa Atiku AbubakarHoto: Atiku Media Office

Atiku Abubakar dai ya nemi kotun ta soke zaben shugaban kasar da ya bai wa Shugaba Muhammadu Buhari nasara. Abubakar da ya taba kasancewa mataimakin shugaban kasa, a yayin mulkin stohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya kalubalanci zaben ne bisa zargin an tabka magudi. Da wannan hukuncin na kotu, ya tabbata cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar cikin watan Fabarairun wannan shekarar. Buhari da ke da shekaru 76 a duniya ya kasance tsohon shugaban mulkin soja a Najeriyar, ya kuma dare kan karagar mulki a karkashin gwamnatin dimukuradiyya a shekara ta 2015 a wa'adi na farko, kafin ya sake tsayawa takara a wannan shekarar inda ya sake lashe zaben da ke cike da tababa.