1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kotu ta kwace wasu kadarorin Madueke

Gazali Abdou Tasawa
October 12, 2017

A Najeriya kotun Tarayya ta birnin lagos ta ba da umurnin kwace wasu gidaje hudu mallakar tsohuwar ministan man fetur Diezani Alison-Madueke a bisa zargin cewa ta mallake gidajen ne ta hanyar kudaden kasa da ta sata.

https://p.dw.com/p/2lizd
Österreich Wien 166. OPEC Konferenz
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Pfarrhofer

A Najeriya kotun Tarayya ta birnin lagos ta ba da umurnin kwace wasu gidaje hudu mallakar tsohuwar ministan man fetur Diezani Alison-Madueke a bisa zargin cewa ta mallake gidajen ne ta hanyar kudaden kasa da ta yi rub da ciki a kansu. 

A lokacin wani zama ne da ta yi a jiya Laraba kotun birnin na lagos ta ba da umurni kwace gidajen wadanda ke a biranan Lagos da Abuja da Port Harcout da darajarsu ta kai ta miliyan bakwai na dalar Amirka.

 Wani bincike da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa ta EFCC ya gano cewa Diezani Alison- Madueke  da wani dan uwanta Donald Chidi Amamgbo sun saye a fakaice wasu manyan gine-gine ta hanyar amfani da wasu kamfanoni na boge.