1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Martanin ofishin Osinbajo kan cecekucen mulki

February 28, 2017

Don kauce wa fito na fito a tsakanin shugaban kasar da mataimakinsa da ke riko a halin yanzu, fadar gwamnatin Najeriya, ta ce ci-gaban da kasar ke samu tsani wanda shugaban kasar ya yi.

https://p.dw.com/p/2YNd8
Nigeria Wahlkampf Mohammadu Buhari & Yemi Osinbajo
Yemi Osinbajo da Shugaba Muhammadu BuhariHoto: picture-alliance/dpa

Kama daga kyautata haske na wutar lantarki ya zuwa ga tsaida ta'annati a yankin Niger delta, dama darajar kudin kasar na Naira da a cikin kwanaki 40 na riko na mataimakin shugaban kasar aka kai ga ganin sauyi a Tarrayar ta Najeriya, abun kuma da ya burge 'yan kasar dama bakinta, sannan kuma ya kai ga abun fadi ga masu adawar da ke fadin kwanaki 40 na Osinbajo sun dara wattanin mulki 20 na Buhari. To sai dai kuma ofishin mataimakin shugaban kasar ya maida martanin cewa duk abun da aka samu a cikin Tarrayar Najeriyar, to yana da ruwa da tsaki da dogon shiri dama umani na shugaban kasar Muhamadu Buhari maimakon siddabaru daga bangaren mataimakinsa da wasu ke kallo.

Kokarin raba kai na shugaba da mataimakinsa

Nigeria Bodo Gemeinde in Ogoni Yemi Osinbajo und Amina Mohammed
Maitaimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo tare da tsohuwar ministan muhalli Amina MohammedHoto: DW/M. Bello

Babban mashawarci na siyasa a ofishin Osinbajo dai ya ce kokarin daukaka mataimakin a kan maigidansa dai na zaman wani yunkuri na tada hargitsi cikin fadar da ta share watattanin 20 a cikin  danyen ganye, ke kuma fatan kai wa ga wasu ba tare da tada hankalin kowa ba. Ko bayan 'yan adawa na jam'iyyar PDP dai, daga dukkan alamu har a cikin jami'yyar APC akwai masu tunanin lallai shugaban yana da abun koyi a bisa salo da tsarin mulkin na Osinbajo.

To sai dai ko ma wanene dalibi a tsakanin shugaban da mataimakinsa dai, karkashin mulkin na tsintsiya dai a fadar mataimakin na shi Osinbajo ai ko mai wala wala bai iya warware matsalolin cikin kasar a cikin kankanan lokaci. A baya dai kokari na zuga yaron a bisa maigidansa dai, ya yi nasarar tada hargitsi a tsakanin tsohon shugaban Tarrayar Najeriya chief Olusegun Obasanjo da mataimakinsa Atiku Abubakar.