1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahawara kan bukatar canza hafsoshin soja a Najeriya

February 19, 2020

A Najeriya a yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar rashin tsaro a kasar, gwamnatin ta ce ba ta da niyyar sauya manyan hafsoshin tsaro akasin bukatar majalisun kasar da ma wasu 'yan kasar ta Najeriya.

https://p.dw.com/p/3Y0yW
Nigeria Präsident Muhammadu Buhari bei Militär in Maiduguri
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Kama daga majalisun kasar guda biyu zuwa sauran 'yan kasa dai batun matsalar tsaro na zaman a kan gaba a daukaci na bukatu na kasar ya zuwa yanzu. Kama daga sashen arewacin kasar ya zuwa na Kudu, ana ci gaba da asara ta rayuka ko dai a cikin hare-haren ta'addanci ko kuma na 'yan ina da kisan da ke kara cin karensu har gashinsa. Abun kuma da ya kai ga tunanin kare wa'adin hafsoshin tsaron kasar da maye gurbinsu duk cikin fatan sabo na zubin na iya kaiwa ga sauyin lamura ga 'yan kasar da ke fadin an mutu an lalace.

To sai dai kuma gwamnatin kasar ta ce ba ta da niyyar sauyin da 'yan kasar ke fatan su gani musamman ma a cikin yanayin da ke kama da babban yaki da kasar ke a ciki a yanzu. Janar Bashir Magashi ministan tsaron kasar ta Najeriya, ya ce har yanzu jagororin yakin na da rawar takawa a kokari na kai ga karshen matsalar da ke zaman ruwan dare gama duniyar kasar.

Nigeria Militär Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: NPR

Damuwa ta mutane ko kuma bukata ta shugaban kasa, hafsoshin dai sun share shekaru hudu maimakon Biyun da ke zaman al'ada ta kasar. Ana kallon dadewa a bisa mulkin tai nasarar toshe kafa ga ragowar hafsoshi da ke da fatan ba da guddunmawa a kokari na kai karshen matsalar ko bayan karewa ta dabarar tsofaffin a tunanin Hon Isa Hassan dake zaman daya a cikin yan doka na kasar.

Nigeria Präsident Muhammadu Buhari bei Militär in Maiduguri
Hoto: Getty Images/AFP/A. Marte

To sai dai koma ya ya take shiri da ta kaya a tunani na gwamnatin da ke fadin ba sauyi, da 'yan kasar da ke tunanin tsufa, hafsoshin da ke a kan gadon dai sun ciri tutar kare bamabamai dama kunar bakin wake da ke zaman al'ada a kasar can baya. Abun kuma da a cewar Bashir Ibrahim bai kamata a manta ba a cikin neman mafita ga kasar da ke ta neman hanyar kai karshen annobar wacce ke rikidewa da shafar sarakuna da ma talakawa na kasar.

Ko a wannan mako dai wasu da ake jin 'yan ina da kisa ne sun hallaka wata jami'a ta mulki a fada ta shugaban kasar a wani abun da ke nuna irin nisan rikicin da ma jan aikin mahukuntan da kansu ke rabe a tsakanin manya na jami'ai na gwamnatin kasar.