1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya na fama da karancin kudade

May 6, 2015

Hukumomi a Najeriya sun nemi bashin kudade daga waje domin biyan albashin ma'aikata sakamakon karancin kudadan da kasar ke fuskanta ta dalilin faduwar farashin mai.

https://p.dw.com/p/1FL4T
Ngozi Okonjo-Iweala
Ngozi Okonjo-IwealaHoto: NICHOLAS KAMM/AFP/Getty Images

Da take magana kan wannan batu Ministan kudin kasar ta Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce suna fuskantar dimbin matsalolin karancin kudi tun daga farkon shekara, kuma tace wannan matsala zata ci gaba da wakana har ya zuwa karshen shekara. Minitar kudin kasar ta Najeriya ta kara da cewa, dama dai gwamnati ta yi nata tsari na karbar bashin da ya kai naira miliyan dubu 882 kwatankwacin Euro miliyan bubu hudu a wannan shekara ta 2015 amma kuma tuni an yi amfani da naira miliyan dubu 473 wajan biyan albashin ma'aikatan gwamnati.

Kasar ta najeriya dai da ke a matsayin wadda tafi ko wace kasa a Afirka arzikin mai, na fuskantar matsaloli tun bayan faduwar farashin danyan mai a kasuwannin duniya wanda kuma kasar ke dogaro da shi da kashi 70 cikin 100.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Pinado Abdu Waba