1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hada kai domin magance rikici a Najeriya

Uwais Abubakar Idris LMJ
July 18, 2018

A karon farko shugabannin manyan kabilu daga sassan Najeriya hudu, sun gudanar da taro a kan asarar rayukan al'umma da ake yi a kasar sakamakon rikice-rikice tare da cimma matsaya ta hada kai domin tunkarar matsalar.

https://p.dw.com/p/31iGB
Niger Kämpfer
Mayakan yankin Niger DeltaHoto: picture-alliance/dpa

Taron dai ya zama tamkar na kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba, saboda yadda dattawa daga yankunan kasar suka rinka kaico na yadda Najeriyar ta kasance a lokacin kuruciyarsu da yadda ta tabarbare a yanzu musamman yawaitar kashe mutane da ma koma bayan rayuwar alumma. Ganawar da ta hadar da shugabannin dattawan Arewa da 'yan kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo da Afenifere ta Yarabawa har da ma 'yan Niger Delta, na zaman muhimmin mataki na kawo karshen zubar da jini a kasar, kamar yadda Farfesa Ango Abdullahi shugaban kungiyar dattawan arewacin Najeriya ya bayyana. Shi ma Mr John Nwodo na kabilar Igbo ya bayyana cewa a yanzu sun fara hakan tattaunawa da wadanda a baya ba sa musayar manufofi da su, domin makomar kasar, inda ya ce za su shiga ko'ina a Najeriya domin tabbatar da sabuwar manufa ga kasa.

Nigeria Angriff von Nomaden im Bundesstaat Plateau | Muhammadu Buhari, Präsident
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yayin ziyarar kokarin warware rikicin jihar PlateauHoto: Reuters/Nigeria Presidency

Hada hannu wajen magance matsala

Kokari na taruwar shugabanin manyan kabilun Najeriya a zaure guda kan wannan matsala dai, na nuna kai wa kowa iya wuya da lamarin ya yi. A nasa bangaren shugaban kabilun yankin Niger Delta ya ce dole ne a fahimci cewa akwai fa matsala, kuma lamura na kara tabarbarewa. To sai dai ga Dr Saidu Dukawa masanin kimiyyar siyasa da ya halarci taron ya ce da gwamnati da ma al'umma baki daya, na da rawar da za su taka. Abin jira a gani  shi ne tasirin da taron zai yi ganin shi ne karo na farko da shugabanin kabilun kasar suka hada kai domin a gudu tare a kuma tsira tare.