1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Nnamdi Kanu ya sake bayyana

Gazali Abdou Tasawa
October 20, 2018

Madugun 'yan awaren yankin Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu wanda ya yi batan dabo yau shekara daya ya sake bayyana a cikin wani faifayin bidiyo a birnin Kudus.

https://p.dw.com/p/36tQ2
Nigeria Biafra | Nnamdi Kanu
Hoto: DW/K. Gänsler

Jagoran 'yan awaren yankin Biafra a Najeriya Nnamdi Kanu wanda ya yi batan dabo yau shekara daya, bayan wani farmaki da sojojin Najeriyar suka kaddamar a gidansa da ke a birnin Umuahia a kudu maso gabashin kasar a ranar 14 ga watan Satumban 2017, ya sake bayyana a cikin wani faifayin bidiyo da aka nada a birnin Kudus. 

Kamfanin dillancin labaran Faransa wanda ya ruwaito labarin a wannan Asabar ya ce a cikin faifayin bidiyon za a iya ganin wani mutum mai kama da Kanun da yafen farin mayafi da kuma hula Kokuwa ta mabiya addinin Yahudu a kansa yana ibada a gaban katangar tuba ta birnin Kudus da ke zama wurin mafi tsarki ga mabiya addinin Yahudu. 

Da dama daga cikin na kusa da shi da kuma lauyansa Ifeanyi Ejiofor sun tabbatar da cewa shi ne a cikin faifayin bidiyon wanda yanzu haka ke yawo a shafukan sada zumunta. Sai dai ya zuwa yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da sahihancin bidiyon.