1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ko PDP da Labour za su kulla sabon aure?

Uwais Abubakar Idris LMJ
March 2, 2023

Kin amincewa da sakamakon zabe ya zama tamkar wata halayyar 'yan siyasa a Najeriya, inda a mafi yawan lokuta suke garzayawa kotu. Tuni jam'iyyun adawa na PDP da Labour, ke shirin kalubalantar sakamakon a gaban kuliya.

https://p.dw.com/p/4OBIz
Najeriya I Atiku Abubakar
Dantakararr babbar jam'iyar adawa a Najeriya PDP, Atiku AbubakarHoto: Pius Utomi Ekpei/AFP

Ba kasafai 'yan siyasar Najeriya ke aminta da sakamakon duk wani zabe da aka gudanar ba, inda da zarar an sanar da sakamakon zabe sukan garzaya gaban kuliya da bukatar a soke ko kuma a juya sakamakon ya zuwa kansu. A zaben wannan shekara na shugaban kasa  ma, manyana jamiyyu uku na adawa da ma wasu daga jamiyya mai mulki da suka yi takara na 'yan majalisu sun bayyana aniyarsu ta yin haka. Sanin kowa ne cewa a zaben na bana an yi amfani da na'urar Bvas da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta bayyana da matakin da ya dakile nau'in magudin zabe a kasar, duk da haka an ga wannan hali na kin amincewa da sakamakon zaben.

Najeriya | Peter Obi
Dantakarar shugaban kasar Najeriya na jam'iyyar Labour, Peter ObiHoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

An dai jima ana koke kan yadda ake daukar dogon lokaci ana shari'o'in zabe a Najeriyar, abin da ke daukar hankalin wadanda ke kan mulki maimakon su mayar da hankali kan aikinsu ga al'ummar da suke jagoranta. Tuni wannan ya fara birkita tsarin zabubbuka a Najeriya musamman na gwamnoni, inda duk da an fara lokaci guda a mataki na kasa a shekar ta 1999 akwai jihohin da ake zabensu a lokuta dabam kaman jihohin Ekiti da Osun da kuma Kogi. Abin jira a gani shi ne shari'ar da za a tafka a kotuna da a yanzu suka zama fage na gaba ga 'yan siyasa da lauyoyi da tuni suka fara shiri domin muhara a shari'o'in zaben. Duk da cewa akwai kotuna na musamman, daga baya ana nufar kotun koli da bisa dole 'yan siyasa ke hakura domin daga ita dole a dangana.