1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kulawa da fannin lafiya a Najeriya

Muhammad Bello/YBFebruary 17, 2016

Wannan na'ura ta jan hankalin ma'aikatan jiyya a asibiti da Chidi ya kirkiro, za ta samar da cigaba a fannin lafiya a kasar ta Najeriya a cewar likitoci.

https://p.dw.com/p/1Hwvj
Bombenanschlag auf Kirchen in Nigeria
Jami'ar lafiya na wa mara lafiya karin ruwaHoto: picture-alliance/dpa

Wani matashi dan Kabilar Igbo a Yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ya samu nasarar kirkiro wata na'ura da za ta iya sanar da cewar ruwan drip na karin ruwa ga mara lafiya,ko kuma jini da ake kara wa mai jinya sun gama shigewa jiki, ta yadda koda Nurse ta yi nisan mita 100 daga gadon mara lafiya, wannan na'ura kan yi sautin sanarwa cewar mara lafiya kaza na bukatar kulawa.

Koda yake akwai kwatankwacin wannan naura a asibitoci,sai dai kuma karin wasu amfani da wannan na'ura ke da shi, likitoci da dama sun tabbatar ta zama abin yabawa.

Matashi Chidi Ohagi dan shekaru 39 an haife shi a kauyen Isouchi da ke karamar hukumar Umuneochi ,a Jihar Abia a shiyar Kudu maso Gabashin Najeriya. Kuma har kawo yanzu,kololuwar makarantar da Mista Chidi ya halarta ,bata wuce sakandare ba.

Nigeria Abuja Maitama Hospital Krankenhaus
Asibiti a NajeriyaHoto: DW

Wannan naurar dai da Ohagi ya kirkiro, ya rada mata suna COHAGI INTRAVENOUS MONITOR,ko CIM a takaice,kuma ga yadda kalmomin suka hadu, Mista Chidi ya zabi makala sunayensa ne don daukar sigar sakamakon kirkirar da ya yi na wannan na'ura.