1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Shirin soma bincike a kamfanin NNPC

Gazali Abdou TasawaAugust 14, 2015

Matakin zai shafi asusunan ajiya na kamfanin na NNPC dama illahirin Kwangilolin aikin man fetir din da Najriyar ta saka wa hannun da kamfanonin da ke aikin hakar man a Ƙasar.

https://p.dw.com/p/1GFfV
Nigeria National Petroleum Corporation Öl-Industrie Korruption
Hoto: Reuters/A. Sotunde

A Najeriya sabon shugaban kamfanin man fetir na Ƙasar Emanuel Kachikwu, ya ba da sanarwar shirin gudanar da binciken asusun ajiya na kamfanin na NNPC . Ya bayyana wannan aniya tasa ce a wata Hira da ya yi da manema labarai a birnin Abuja, inda ya ce matakin zai kasance na ba sani ba sabo da zai bincike hatta Ƙananan ma'aikatan kamfanin. Kuma shirin zai shafi shekara ta 2014 da ta 2015 dama kuma illahirin kwangilolin na raba arzikin man fetir da ƙasar ta Cimma da kamfanonin da ke aikin haƙar man fetir a ƙasar ta Najeriya.

A farkon wannan wata na Ogusta ne dai Shugaban ƙasar ta Najeriya Muhamadu Buhari ya kori tsaffin shugabannin kamfanin na NNPC tare da naɗa masa sabon babban darakta da nufin tsarkake kamfanin . Najriya dai wacce ke hako ganga miliyon biyu ta man fetir a ko wane yini na a matsayin ƙasa ta farko wajan arzikin man fetir a Nahiyar Afirka. Kuma shi ne kashi 90 daga cikin dari na hajojin da ƙasar ke sayar wa a ƙasashen ƙetare.