1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta ɗauki kofin ƙwallon Afirka karo na uku

February 11, 2013

'Yan Najeriya masu sha’awar ƙwallon ƙafa na ci gaba da bukukuwan samun nasarar lashe gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na ƙasashen Afirka.

https://p.dw.com/p/17c6r
Nigeria's players celebrate winning their African Nations Cup (AFCON 2013) final soccer match against Burkina Faso in Johannesburg February 10, 2013. REUTERS/Siphiwe Sibeko (SOUTH AFRICA - Tags: SPORT SOCCER)
Hoto: Reuters

Tun daga fadar shugaban Najeriyar, zuwa ga Majalisar Dattawa har zuwa talakan ƙasar saƙo ne na yabo da jinjinawa 'yan wasan na Najeriya, abinda ya sanya Hon Rigajichukun bayyana yadda suka ɗauki lamarin, musamman ganin tawaga mai ƙarfi daga majalisar ta yi takaka zuwa Afrika ta kudu domin kallon wasan.

Duk da cewa litini ranar ce ta aiki a Najeriya, amma fuskokin jama'a musamman matasa sun kasance cike da annuri na samun nasarar gasar, kuma ma babu wani batu da ake tattaunawa a kansa da ya wuce ba nasarar da ƙungiyar ta Super Eagles ta samu, musamman ganin yadda suka fara wasa a gasar. Ga dai ra'ayoyin wasu mazaunan birnin na Abuja.

Yace gaskiya na ji daɗi sosai musamman ganin cewa tun 1994 rabon da Najeriya ta ɗauki wannan kofi. Duk wani ɗan Najeriya da ya cika ɗan Najeriya ya bayana jin daɗin cewa Najeriya ta ci wannan gasar na nahiyar Afrika, koda yake a lokacin da aka fara wannan gasa, bamu ba ita ƙungiyar Super Eagles da ma cewa za ta ci kofin ba amma gashi ta samu nasara don haka ina murna. Abinda wannan ke nufi shine ƙwallon Najeriya na nan daram kuma in aka cire siyasa ƙwallon nan nan kamar yadda take a da. Ta ce ina murna da cin ƙwallon da Najeriya ta yi domin Najeriya ta daɗe ba ta ci ƙwallo ba sai wannan shekara a gaskiya ina murna''.

Nigeria's forward Brown Ideye (back) attempts to score past Burkina Faso's defender Bakary Kone (C) and Burkina Faso's defender Mady Panandetiguiri during the 2013 African Cup of Nations final football match between Burkina Faso and Nigeria on February 10, 2013 at Soccer City stadium in Johannesburg. AFP PHOTO / ALEXANDER JOE (Photo credit should read ALEXANDER JOE/AFP/Getty Images)
Hoto: Getty Images

Mazauna birnin Abuja hedikwatar Najeriya sun kasance cike da murna da bukukuwa na samun nasarar lashe gasar cikin kofin ƙasashen Afrika da Najeriya ta yi bayan kwashe shekaru 19 a jere tana ƙoƙarin maimaita tarihin da ta yi a ƙasar Tunisiya a 1994.

Irin rawar da ƙwallon ƙafan ke takawa a Najeriya a matsayin wacce ke ɗinke duk wata ɓaraka ta bambancin addini ko ƙabila da ta yi ƙaurin suna a ƙasar.

A yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da bukukuwa da ma sa idon dawowar 'yan wasan na Super Eagles daga ƙasar Afrika ta kudu, ga Gboyega Adeniran mai sharhi a fanin ƙwallon ƙafa ya ce akwai muhimmin abu da ke tattare da nasara da Najeriya ta samu, musamman sanin cewar an garwaya 'yan wasa da ke a wasanin rukuni-rukunin Najeriyar wajen wannan gasa.

Yace: wannan nasara ta kara nuna cewa in Najeriya ta yi amfani da alƙalan wasa da 'yan wasa na cikin ƙasarta ba sai mun ɗauko wani coach daga ƙasashen Turai ba, domin wannan ya ƙara tallafawa 'yan wasan kansu don a nunawa duniya cewa nan Najeriya fa ana ƙwallo, sannan wannan wasa ya ƙara kawo zumunci don zaka ka a unguwani da dama ana ta murna ana jin daɗi, don haka ya ƙara kawo haɗin kai''.

epa03570880 Nigeria players celebrate after Elderson Echiejile (L) scored the first of three first half goals during the semi-final match in the Africa Cup of Nations between Mali and Nigeria played at The Moses Mabhida Stadium, Durban, South Africa, 06 February 2013. EPA/KIM LUDBROOK +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Murna bisa murna dai ga Najeriya shine baya ga zama zakarun Afrika, ƙasar zata yi tsayuwar tsara da sauran zakarun ƙasashen duniya a gasar cin kofin confederation na FIFA da za'a yi a ƙasar Brazil.

A 1980 ne dai Najeriya ta fara lashe gasar ta cin kofin ƙasashen Afrika, inda saida ƙasar ta kwashe shekaru 14 kafin ta sake lashe kofin a Tunisiya a 1994, sannan yanzu kuma a Afrika ta kudu.

Mawallafi:Uwais Abubakar Idriss
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani