1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta buƙaci agajin Amirka

Muntaqa AhiwaFebruary 14, 2015

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi kiran agajin ƙasar Amirka kan yaƙi da Ƙungiyar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1Ebu6
Nigeria Goodluck Jonathan
Hoto: AFP/Getty Images

Shugaban na Najeriya da ya nuna buƙatar taimakon Amirka kan batun na Boko Haram, ya bayyana matsayinsa ne a hirar da ya yi da jaridar Wall Street Journal, inda a karo na farko ya fito ya danganta Ƙungiyar ta Boko Haram da Ƙungiyar IS da ke ƙasashen Syria da Iraƙi.

Mr. Jonatahna ya ce idan Amirka za ta taimaka wajen yaƙar Ƙungiyar IS, to babu dalilin da zai hana ta taimaka wa Najeriya ta yaƙi Boko Haram.Kallaman na Jonathan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da mayaƙan na Boko Haram suka afkawa garin Gombe da ke a arewa maso gabashin Najeriya.

Mawallafi : Muntaqa Ahiwa
Edita Abdourahamane Hassane