1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya ta yi gargadi da a guji yin sakaci a yaki da Ebola

August 27, 2014

Wannan gargadin ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa wasu 'yan Najeriya sun fara shagulgulan samun nasara kan cutar.

https://p.dw.com/p/1D2o5
Onyebuchi Chukwu Nigerias Gesundheitsminister 14.08.2014
Hoto: Reuters

Ministan kiwon lafiya na Najeriya, Onyebuchi Chukwu a wannan Larabar ya yi gargadi da a guji yin sakaci a yakin da kasar ke yi da cutar Ebola, duk da cewa mai jinya daya da ke dauke da kwayar cutar ya rage a asibiti. A ranar Talata ministan ya sanar cewa an sallami karin mutum biyu daga kebabben wurin da ake musu magani, abin da ya kawo yawan marasa lafiya da aka yi nasarar warkar da su daga cutar ya zuwa mutum bakwai. Mutane biyar suka rasu a Najeriya tun lokacin da aka shiga mata da cutar a ranar 25 ga watan Yuli. Ministan ya kuma yi kashedi da a guji buga labaran taya murna cewar an kawar da kwayar cutar a Najeriya. Gargadin ministan na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa wasu 'yan kasar sun fara shagulgulan samun nasara kan cutar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Abdourahmane Hassane