1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin gwamnatin Najeriya kan kisan ma'aikaciyar agaji

October 16, 2018

Martanin kan kisan ma'aikaciyar agaji ta biyu cikin wata guda a bangaren kungiyar Boko Haram wanda gwamnatin Najeriya ta yi  tir da kisan da ta kira na rashin imani a bangaren kungiyar tsagerun mai dauke da makamai.

https://p.dw.com/p/36dXD
Nigeria Rotes Kreuz
Hoto: Getty Images/AFP/A. Emmanuel

Kama daga ita kanta fadar gwamnatin kasar ta Aso rock ya zuwa 'yan fafutuka da hedikwatar kungiyar Red Cross dai hankula sun tashi bayan labarin halaka Hauwa Liman da kungiyar Boko Haram ta aikata.

Kungiyar dai ta halaka jami'ar 'yar shekaru 24 da haihuwa kuma ta biyu a cikin tsukin wata guda a bangare na Boko Haram da ke neman karin tattaunawa da gwamnatin.

Kisan dai na kara fitowa fili da irin jan aikin da ke gaban Najeriya da ke fadin tai nisa a kokari na kare matsalar amma kuma ke kallon tasirinta na kara karuwa cikin kasar.

Hauwa Mohammed Liman
Marigayiya Hauwa Mohammed Liman da tsagerun suka kashe a NajeriyaHoto: Reuters/ICRC

Liman din dai na zaman daya a cikin ma'aikata na agaji guda ukun da kungiyar ta sace bayan wani samame da ta kai a sansanin 'yan gudun hujirar da ke garin Ran a Jihar Borno. Kuma a watan Satumban da ya gabata ne Boko Haram ta halaka Saifura Ahmed da ke zaman daya a cikin guda uku kafin halaka Liman.

Mallam Garba Shehu na zaman kakaki na gwamnatin da ya ce ta yi baki ta yi duhu ga Abuja ta dauki duk matakai amma kuma ta kare ba nasara a kokari na ceto Liman.

Majiyoyin fadar gwamnatin kasar sun ce an tsara shugaban kasar zai buga waya domin yin ta'azziya ga mahaifin ita Liman nan gaba.

Nigeria CJTF-Hauptquartier in Maiduguri
Hoto: Imago/Zuma Press

To sai dai kuma kisan ya jawo wata zanga-zangar bacin rai a bangare na 'yan kungiyar "Bring Back Our Girls" da suka yi tattakin nunin alhini zuwa fadar gwamnatin kasar suka kuma ce shugaban kasar ya kasa.

Ibarhim Morocco dai na zaman daya a cikin 'yan kungiyar da ke fadin babu gaskiya cikin hasashe na gwamnatin kasar a bisa kokari na ceto Liman.

To sai dai kuma offishin na Red Cross da ke Abuja dai sun ce har yanzu suna zaman jira na tabbacin kisan na Hauwa Liman daga hedikwatarsu da ke kasar Switzerland kafin mayar da martanin da ya dace. Babu dai wata sanarwa daga ita kanta kungiyar ta Boko Haram game da kisan a wani abin da ke zaman ba sabon ba.