1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya tana nasara a yaki da ta'addanci

Uwais Abubakar Idris/USUSeptember 3, 2015

Rundunar sojan kasar ta ce tana samun gagarumin ci gaba a fafatawa da kungiyar Boko Haram ta kuma dawo da sojoji sama da 3000 daga cikin 5000 da aka kora a baya

https://p.dw.com/p/1FM2Y
Nigeria Armee Operation gegen Boko Haram
Hoto: picture-alliance/dpa

To nasarorin da rundunar sojan Najeriyar ta bayyana cewa tana samu a ‘yan kwanakin nan a yaki da take da masu kai hare-hare musamman a Arewa maso Gabashin kasar, da a yanzu wa’adin da shugaban kasar ya basu na kawo karshen matsalar nan da watani uku, ta sanya sojojin bayyana ganin haske a wannan aiki da a lokutan baya ake ganin ya nemi kaisu dare.

Kama daga kwato garin Gambouru Ngala daga hannun ‘yayan kungiyar ta Boko Haram, ya zuwa kara kaimi ga kai hare-hare a gadun dajin Sambisa da sojoji suka samu lalata hanyar samar da wuta lantarki ga yayan kungiyar, har ma da gano cibiyar da suke harhada makamansu, duk bayanai ne da suke tinkaho da su. To shin me ya hana su samun wannan ci-gaba a lokutan baya? Kanal Sani Usman Kuka Sheka shi ne mukadashin daraktan yada labaru na rundunar sojan Najeriyar, ya kuma bayyana cewa.

"Mun samu karin sojoji, mun samu karin kayan aiki da makamai. Sannan kuma akwai wani sabon hadin kai na danganatakar juna bama ga jami’an tsaro ba, har ga kasashen da muke makwabtaka da su. Domin wannan matsala ce da wuta taki cinyewa, don haka aka hada karfi muke samun nasara, don haka kwanan nan zamu samu kawo karshen wannan matsala."
To ko wane tasiri wannan zai yi ga tarba –tarbar da ake ci gaba da yiwa wannan matsala? Malam Kabiru Adama kwararre ne a fanin harkokin tsaro a Najeriyar.
"Muhimmin abubuwa wanda mu da muka ji dadi wuraren hada bama-baman nan da muka gano, in har aka gano tushen matsalar, muna sa ran za’a shawo kanta nan gaba kadan."

To sai dai duk da wannan nasara da rundunar sojan Najeriyar ke bayyana cewa ta samu da ma bada tabbacin cima wa’adin watani uku, da aka bata na kawo karshen matsalar. Har yanzu ana ci gaba da fuskantar masu kai hare-haren da ke canza salo a kan jama’a. Har ila yau ga Kanal Sani Usman Kuka-Sheka.

"Saboda farmakin da ake kai masu, duk inda aka san ‘yan Boko Haram suke musamman kasan sojojinmu na sama suna amfani da jirage suna sakan masu bama-bamai a dajin Sambisa, to wadanda yunwa ta dame su ana samun su suna fita kuma. Ka san suna da makamai to suke kai hare-hare."

A yayinda sojojin ke kara zage damtse a yakin da suke yi a cikin kasar, rundunar sojan ta sanar da maido na sojoji 3,032 bakin aikinsu, daga cikin sojoji 5000 da aka kora saboda laifuffuka iri daban daban, sai dai wadannan basu hada da wadanda aka yankewa hukunci kisa ba.

Kama hanyar shawo kan matsalar dai na zama abinda ke jan hankalin al’ummar Najeriyar, musamman wadanda suka baro gidajensu da ke zura idanu lokacin da za su koma don ci gaba da rayuwarsu.