1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'addanci na kamari a jihohin Borno da Yobe

June 18, 2019

Ana samun koma baya dangane da harkokin tsaro a shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya inda mayakan Boko Haram ke kai hare-hare ba kakkauta wa a sassan jihohin Borno da Yobe.

https://p.dw.com/p/3KeJm
Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

Ra’yoyin jama'a dai sun sha bamban kan musabbabin zafafa hare-haren da mayakan na Boko Haram ke yi,  inda wasu ke zargin sakacin gwamnati wasu kuma ke ganin mayakan na Boko Haram na kara nuna karfin su ne don karyata ikirarin sojoji da ke cewa sun gama da su. Lamari ne da ya haifar da asarar rayuka  na fararen hula da tarin dukiyoyi da kuma tilastawa dubbai barin gidajensu.

Nigeria Selbstmordattentäter greifen Hilfs-Zentrum in Maiduguri an
Hare-haren Boko Haram sun kara kamari a jihohin Borno da YobeHoto: picture alliance/dpa/AP Photo/H. Suleiman

A  bayan-bayan nan, harin kunar bakin wake da aka kai garin Konduga mai nisan kilomita 25 daga birnin Maiduguri ya yi sandiyar mutuwar mutane sama da 30 da kuma wanda mayakan Boko Haram suka kai a kauyen Molai mai nisan kilomita 7 daga birnin duk a ranar Lahadin da ta gabata. Kan ko me ya janyo wannan sabon tashin hankalin dai, ra’ayoyin mutane sun sha bamban sai dai da dama sun fi raja’a kan cewa mayakan na Boko Haram na son nuna karfin ikon da su ke da shi ne yayin da wasu ke cewa, rashin farautar mayakan zuwa tungarsu da sojojin Najeriya ba sa yi ne ke ba su damar kai wadannan hare-haren.

Nigeria Maiduguri Trauernde nach Boko Haram Attacke
Jama'a da dama na zargin gwamnati da yin sakaci a yaki da Boko HaramHoto: Getty Images/AFP/A. Marte

Abin da ya bayyana a fili dai shi ne, hare-haren na jefa tsoro da fargaba ga al’umma ba kawai wadan ke zaune a yankunan karkara da tsaro bai inganta ba har ma da wadnda ke zaune a birnin Maiduguri da ake ganin akwai cikakkun matakan tsaro. Tashe-tashen hankualn na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya sabunta wa’adin manyan hafsoshin tsaro na kasar duk da kiraye-kirayen sauya su a samu sabbin jini da za su fuskanci matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta na tsawon lokaci da jama'a suka yi.