1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tallafin dalibai ga yara 'yan gudun hijira a Najeriya

Ibrahima YakubuJune 22, 2016

Daliban manyan makarantun Najeriya sun bullo da tsarin ilimantar da yara da sauran marayu a sansanonin 'yan gudun hijira da ke a arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/1JAjW
Entwicklungshilfe Afrika
Hoto: picture-alliance/dpa

Hadaddiyar Kungiyar Daliban Manyan Makarantun Najeriya ta bullo da wani sabon salon ilmantar da kananan yara marayu 'yan gudun hijira a sansanin 'yan gudun hijirar wadanda aka kwaso daga Arewa maso Gabashin kasar. Yanzu haka wadannan yara suna zama tare da daliban a cikin makarantunsu domin horar da su ta hanyar wani tsarin kararun da suka kirkiro da suka yi lakabin "Up-Camp Education System" da zai ba su damar sanya su a wasu makarantu. Wannan matakin na da zumar magance karancin ilimi da ke addabar miliyoyin kananan yara marayu 'yan gudun hijira.

Mr. Adikpee Odeh shi ne shugaban daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic, da ke bayyana cewa:

"Dole ne mu tashi tsaye domin tabbatar da ganin cewa mun bayar da ta mu gudunmawar a kan ceto dubban kananan yara marayu 'yan gudun hijira da ke matukar fama da matsalar jahilci. Muna ganin cewa akwai hanyoyin da za mu ba da gagarumar gudunmawa ta hanyar kirkiro wasu hanyoyin ilimantar da wadannan yara da kuma tabbatar da ganin cewa dukkanin 'yan Najeriya sun bada ta su gudunmawar a kan ilimin wadannan yara domin magance yiwuwar kara bullar duk wata kungiya da ke adawa da ci-gaban alumma."

Ilimi da sana'ar hannu don dogaro da kai

Baya ga haka ma dai har wa yau akwai wani tsarin karantarwa da daliban suka bullo da shi mai suna "Adopt a Refugee Child & Education" wato daukar dawainiyar yaro dan gudun hijira kama tun daga iliminsa da ciyarwa tare da tufafinsa da kuma horar da su wasu kananan sana'o'in hannu don su zamo masu dogaro da kansu a nan gaba.

Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
Hukumar taimakon gaggawa a Najeriya ta kafa cibiyoyin koyar da yara 'yan gudun hijiraHoto: Reuters/S.Ini

Bugu da kari Kungiyar daliban yanzu haka na tattara miliyoyin takardu daga hannun 'yan Najeriya da ake rarraba wa sauran kananan yara 'yan gudun hijira a sansanoni daban daban da ke a yankin Arewa maso Gabashin kasar domin kowane dan Najeriya ya bada tasa gudunmawar a kan ilimin marayun.

"Donate a Book Campaign for Refugee Child Education" a cewar shugaban daliban Adikpee Odeh ya samu karbuwa daga 'yan kasar.

Ya ce: "Mun yi kira ga 'yan Najeriya kuma sun amsa kiran da muka yi masu na su bayar da kyautar tsaffin takardun karatunsu domin taimaka wa fannin ilimin kananan yara marayu. Mun samu takardu sama da miliyan daya kuma mun riga mun aika da su jihojin Arewa maso Gabashin kasar."

Hannu daya ba ya daukar jinka

Kungiyar daliban dai ta dauki nauyin karatu wadannan yara tare da hadin guiwar wasu makarantu masu zaman kansu inda suke koyar da yaran a kyauta.

Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
Raba abinci na daga cikin ayyukan tallafa wa 'yan gudun hijiraHoto: Reuters/S.Ini

Cikin yara marayu da daliban suka dauko daga jihar Borno ga abunda yake cewa:

Ya ce: "Ana koya mana lissafi da turanci da kimiyya da kuma fannin addini. To sai dai ina bukatar "uniform" da takalmi da rula da sauran abun karatu da zai taimaka mani wajen dukufa yin karatu kamar sauran kananan yara."

Mallam Ibrahim Yaba ya dai kasance daya daga cikin 'yan Najeriya da ya bada kyautar wasu tsaffin takardunsa don a rarraba wa wadannan yara 'yan gudun hijira:

Ya ce: "Aabun mamaki ne yadda dalibai daga Kaduna suka je Borno domin dauko kananan yara marayu don ba su ilmi. Amma abun takaici a nan shi ne yadda hamshakan 'yan Najetiya suka gaza wajen bada tallafi ga bangaren ilimin kananan yaran 'yan gudun hijira."

Yawancin wadannan yara marayu da daliban manyan makarantun kasar ke kulawa da su, yara ne da Boko Haram suka hallaka iyayensu a gaban su, da yanzu haka ake tallafa masu don su zamo mutane na gari.