1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nakiyoyi sun tashi a Fatakwal, Nigeria

April 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1Q

Kungiyyar dake gwagwarmayar kwatowa yan yankin Niger Delta a tarayyar Nigeria yancin su, wato Mend, tace itace ta dana nakiyoyin da suka tashi a jikin wata mota da aka ajiye kusa da wani barikin soji dake birnin Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers.

.Kungiyyar ta Mend ta fadi hakan ne a yau ,a cikin wani sako data aike izuwa yanar giza gizan sadarwa na duniya, wato Internet a turance.

Wannan dai kungiyya ta Mend data dade da yin kaurin suna wajen dauki ba dadi da jami´an tsaro a yankin na Niger Delta, ya zuwa yanzu bata fadi dalilin kai wannan hari ba.

Wannan mummunan aiki dai ya zuwa yanzu a cewar rahotanni yayi sanadiyyar rasuwar mutane biyu, wasu kuma kalilan sun jikkata