1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da gwabza fada a garin Sirte

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 22, 2016

Dakarun soja da ke goyon bayan gwamnatin hadaka ta kasar Libiya, sun samu nasarar kwace iko da wasu sassa na garin Sirte da ke zaman babbar tungar 'yan ta'addan kungiyar IS.

https://p.dw.com/p/1JBXF
Fafatwa Domin kwace garin Sirte daga IS
Fafatwa Domin kwace garin Sirte daga ISHoto: picture alliance/abaca/AA

Kungiyar IS dai na neman mamaye kasar Libiya. Rahotanni sun nunar da cewa dakarun sun samu nasarar kwace iko da wata babbar hanya da kuma gidan radiyo na garin na Sirte a wani gagarumin bata kashi da suka yi da mayakan kungiyar ta IS. Ko da yake rundunar sojojin na Libiya ta yi asarar a kalla sojoji 84 tun bayan fara gwabza fada tsakaninsu da mayakan na IS a ranar Talatar da ta gabata yayin da wasu 135 suka jikkata, sun samu gagarumar nasara a wannan arangama. Rundunar sojojin ta Libiya dai ta sanar da cewa tun bayan da suka fara fafatawa da 'yan IS din cikin watan da ya gabata kawo yanzu, sojoji 220 ne suka halaka.