1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

NATO na shirin kaddamar da atisaye mafi girma

Binta Aliyu Zurmi
January 18, 2024

Kungiyar kawancen tsaro ta NATO na shirin kaddamar da wani atisaye mafi girma a tarihin kungiyar da ya kunshi sojoji dubu 90,000 da nufin dakile duk wata barazanar tsokana da ka iya tasowa daga bangaren Rasha.

https://p.dw.com/p/4bQqa
NATO-Generalsekretär Jens Stoltenberg besucht der Premierminister von Nordmazedonien Dimitar Kovacevski
Hoto: Petr Stojanovski/DW

Wannan atisayen da ke zama irinsa na farko tun bayan yakin cacar baka, a cewar kungiyar ta NATO na zama na kariya ne ga kasashe mambobinta musamman ma wadanda ke kusa da kasar Rasha.

Kasashen Estonia da Latvia da Lithuania gami da Poland na a sahun gaban kasashen NATO da ke kallon kansu a matsayin barazana daga mamayar Rasha kanancewar kusancin kasashen da ita.

A cewar NATO wadannan kasashen ka iya wata rana su tsinci kansu a halin da Ukraine ke ciki a yanzu, hakan na daga cikin dalilin da ya sa dole su dauki mataki.

A watan Fabarairu ne ake sa ran kaddamar da wannan atisayen, wanda kasar Burtaniya da ke zama guda daga cikin mambobinta ta tabbatar da cewar sojojinta da suka hada da na sama da na kasa gami da na ruwa dubu 20,000 ne za a fafata da su.

Karin bayani: NATO: Kammala atisayen sojin sama