1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Navi Pillay ta fara ziyara a Sudan ta Kudu

April 28, 2014

Shugabar hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ta isa Sudan ta Kudu don duba halin ake ciki a kasar bayan kisan da aka yi.

https://p.dw.com/p/1BqT3
UN Navi Pillay in Bangui 20.03.2014
Hoto: Reuters

Ms. Pillay da mazon Majalisar Dinkin Duniya na musamman mai kare kisan kare dangi Adama Dieng za su tattauna da Shugaba Salva Kiir da wasu manya 'yan siyasar kasar, baya ga ziyarar gani da ido da za su kai wuraren da aka yi kashe-kashen.

A makon da ya gabata dai kwamitin sulhu ma Majalisar Dinkin Duniya ya yi barazanar sanya takunkumi ga wadandan ke da hannu kan rikicin Sudan ta Kudun musamman ma dai dakarun gwamnatin Shugaba Kiir da 'yan tawaye da ke goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Pinado Abdu-Waba