1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman hanyoyin ingata lamura a Somaliya

October 29, 2014

Jakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban da shugaban Bankin Duniya sun kai ziyara zuwa kasar Somaliya

https://p.dw.com/p/1Ddqk
Hoto: Getachew Tedla HG

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya kai ziyarar aiki zuwa Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, inda ya gana da Shugaba Hassan Sheikh Mohamud karkashin tsauraran matakan tsaro.

Ban tare da Shugaban Bankin Duniya Jim Yong Kim suka kai ziyarar inda suka gana da Shugaba Sheikh Mohamud a filin saukan jiragen sama, wanda dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayar Afirka da ke samun tallafin Majalisar Dinkin Duniya ke gadi. Fadar shugaban kasar ta Somaliya ta ce ganawar tana da nasaba da kara inganta lamura a kasar da yaki na tsawon shekaru ya wargaza.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu