1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Neman mafita daga matsalolin Najeriya

November 6, 2013

Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Najeriya ta gudanar da taronta karo na shida, don tattauna batutuwan da suka shafi samun hadin kai da tsaron da ya tabarbare a kasar.

https://p.dw.com/p/1AD6z
Hoto: Sultan's Office

An dai dan samu mabambantan ra'ayoyi a tsakanin sarakunan gargajiyar dangane da samar musu matsayi a kundin tsarin mulkin kasa, wanda hakan ke nuni a fili da cewa har yanzu kan masu rike da sarautun gargajiyar bai zamo guri guda ba a kan batun. Taron da suka gudanar a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriyar, ya samu halartar kakakin majalisar dokoki ta kasa Aminu Waziri Tambuwal, wanda ya shaida wa taron kokarin da majalisar take na ganin an dama dasu wajen mulkin kasa, tare kuma da yin bayanin matsayin da suka cimma.

Sai dai a jawabinsa, Lamidon Adamawa Dakta Muhammad Barkindo, ya nunar da cewa sarakunan gargajiya ba sa bukatar wani matsayi a tsarin mulkin kasa, inda yace dama suna da matsayi tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka.

Nigeria Emirs-Palast Katsina
Fadar sarkin Katsina, a Najeriya.Hoto: DW

Shi kuwa a nasa jawabin, mai alfarma sarkin Musulmi Dakta Sa'ad Abubakar na uku, kuma shugaban majalisar, ya tunasar da sarakunan gargajiyar cewa aikin samar da cigaban hadin kan Najeriya wuri guda, aiki ne da suka gada, kuma dole su ci gaba da tabbatar da shi.

Yace "Tun kafin kafuwar Najeriya, masu rike da sarautun gargajiya ke gudanar da mulki, wanda kowa ya sani a tarihi kuma ya kamata kowa ya rinka karatun tarihin, don shi kawai zai bamu damar ci gaba da hada kai domin zama abu guda, sarautun gargajiya su ne kadai ke hada kan 'yan kasa har ya zuwa yanzu, kuma muna ba gwamnatin Tarayyar Najeriya tabbacin ci gaba da bada goyon bayanmu ga dorewar Najeriya wuri daya".

A jawabinsa na bude taron, shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda mataimakinsa Alhaji Namadi Sambo ya wakilita, ya sake jaddada irin goyon bayan da suke bukatar masu rike da masarautun gargajiya su kara basu wajen ganin an samar da tsaro da kuma kare lafiya da dukiyar 'yan kasa.

Nigeria Vizepräsident Namadi Sambo
Mataimakin shugaban kasa a Najeriya Alh. Namadi SamboHoto: AFP/Getty Images

Yace "Aikin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyar 'yan kasa, aiki ne da ya rataya a wuyan gwamnati, amma kuma duk da haka muna neman saka hannun bangarori da dama irin su sarakunan gagrgajiya, masu fada a ji da kuma kungiyoyin fararen hula domin cimma burin, wanda in mun samu hakan Najeriya za ta kai inda kowace kasa ta kai a wajen cigaba".

Taron dai zai tattauna sakamakon rahoton kwamitin da majalisar ta kafa a 'yan watannin baya da aka baiwa alhakin nemo hanyoyin magance rashin tsaro da ke addabar wasu sassa na Najeriya da kuma lalubo mafita ga ci gaban hadewar Najeriya a wuri guda.

Mawallafi: Aminu Abdullahi Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh/ LMJa'afar

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani