1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nicolas Maduro ya lashe zaben Venezuela

April 15, 2013

Babban kalubalen dake gaban sabon zababben shugaban kasar shine farfado da tattalin arzkkinta da kuma jan hankalin yan adawa zuwa ga manufofinsa

https://p.dw.com/p/18GJz
Hoto: Reuters

Dan takarar da marigayi  Hugo Chavez ya zabe shi  a matsayin magajinsa a shugabancin Venezuela, wato  Nicolas Maduro, shine  kuma ya smai nasarar zaben da aka  gudanar a kasar  a wannan mako. To sai dai rahotanni sun nuna cewar  Maduro da kyar ya tsallake rijiya da baya, saboda rinjayen da ya samu bai taka kara ya karya ba a zaben na shugaban kasa a kan abokin adawarsa, Henrique Capriles, wanda ya tsaya a madadin jam'iyun adawa.

Nasarar a  dan takarar na magoya bayan Chavez, ta biyo bayan  kazamin kampe ne da yan takarar guda biyu suka gudanar kafin zaben, inda  Maduro yayi alkawarin ci gaba da bin  manufofin Hugo Chavez idan aka zabe shi, shi kuma abokin takarar sa Capriles yayi alkawarin maida Venezuela kan takarfi mai karfi, bayan da Chavez ya maida Venezuela, daya daga cikin kasashen da suka fi arzikin man fetur a duniya kan tafarkin rushewarta. Shi kansa Maduro ba bako bane a yanayin mulkin kasar, saboda ya  rike mukamin shugaba na rikon kwarya tun da Chavez ya mutu ranar 5 ga watan Maris.

To sai dai a yayin da magoya bayan  Chavez da Maduro suke murnar wannan nasara da dan takararsu ya samu, dan adawa Capriles  ya nemi a gudanar da bincike mai tsanani game da sakamakon zaben, kuma idan hali ya kama,  har ma a sake kidaya kuri'un gaba daya, ganin cewar tazarar dake tsakanin yan takarar biyu bata wuce ta kuri'u dubu 235 ba. Bayan da Venezuela ta zama kasa mai cinikin man fetur a duniya,  'ya'yanta da yawa sun fita daga mummunan hali na talauci, to amma daga baya yan adawa sun zargi magigayi Chavez da laifin komawa gidan jiya, inda gwmanatinsa ta kasa ciyar da  al'ummarta, duk da dimbin arzikin mai da take dashi. Wani masani kan kasar ta Venezuela, Stefan Peters na jami'ar Kassel yace:

Venezuela Henrique Capriles zeigt knappen Verlust an
Wakilin jam'iyun adawa Henrique CaprilesHoto: Reuters

"Kasar ta kasa samun nasarar janye kanta daga dogara gaba daya kan tsarin tattalin arzikin da ya dogara gaba daya kan man fetur, tare da karfafa wasu hanyoyin dabam na aiwatar da kayaiyaki a wannan kasa."

Bayan nasarar da  Maduro ya samu, yanzu dai  abin da za'a zura ido a gani shine ko  sabon shugaban  zai dan kauce daga manufofin Chavez, yadda zai kyautata hanyoyin rabon arzikin kasar ta venezuela. Masana suka ce basu ga alamun hakan zai samu ba, domin kuwa a yanzu haka yan kasar suna  fama da hauhawar farashin kaya da ya kai kashi 20 cikin dari, yayin da masana'antunta suke kan hanyar rushewa gaba daya. A watan Fabrairu sai da ya zama tilas  kasar ta rage darajar kudinta, saboda  abin da take samu daga ketare bai kai yadda take bukata domin biyan dimbin bashin dake kanta ba, duk kuwa da sanin cewar Venezuela din tana daya daga cikkn kasashen da suka fi arzikin man fetur a duniya. Stefan Peters na jami'ar Kassel yace:

"Duk da wannan dimbin arziki, amma Venezuela tilas  taci gaba da shigo da kayan abinci daga ketare, saboda  babu wata hanya dabam ta samarwa al'ummar kasar isasshen abinci. Kayan abinci da kasar ita kanta take nomawa ya ja da baya matuka. Burin da gwamnati ta daukarwa kanta na kasancewar mai cikakken yancin a fannin samar da abinci, ba zai tabbata a zahiri ba nan gaba kadan."

(121014) -- CARACAS, Oct. 14, 2012 () -- Venezuelan President Hugo Chavez speaks during the swearing in ceremony of Vice President Nicolas Maduro and six cabinet ministers at Miraflores Palace, in Caracas, Venezuela, on Oct. 13, 2012. (/AVN) (dzl)
Marigayi Hugo Chavez ya mutu ya bar baya da kuraHoto: picture-alliance/Photoshot

Duk da adawa da  kiraye-kirayen da  jam'iyun adawa suka yi na sake kidaya kuri'u a zaben ranar Lahadi, amma  yau da yamma hukumar zabe ta tabbatar da Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben, yayin da gwamnati ta shirya gagarumin taro a birnin Caracas, domin bikin nasarar da  magajin na Chavez ya samu.

Mawallafi: Umaru Aliyu
Edita: Yahouza Sadissou