1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Bude zaman taron shugabannin AU

Gazali Abdou Tasawa
July 7, 2019

Shugabannin kasashen Afirka na kaddamar a wannan Lahadi da yarjejeniyar cinikayya maras shinge a tsakanin kasashen a taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka da ke gudana a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar. 

https://p.dw.com/p/3LheI
Äthiopien AU-Gipfel in Addis Adeba
Hoto: Getty Images/AFP/M. Tewelde

Mutane kimanin dubu hudu ne da suka hada da shugabannin kasashe 32 da ministoci sama da dari ke halartar taron na birnin Yamai. Wannan yarjejeniyar kasuwanci maras shinge ta CFTA ko ZLEC na da burin bunkasa huldar cinikayya ta tsakanin kasashen Afirka 55 daga kaso 13 daga cikin dari da take a halin yanzu zuwa kaso 60 daga cikin dari nan zuwa shekara ta 2022. 

Najeriya da ke zama kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar da kuma ta jima tana dari-darin shiga a cikin shirin, za ta sanya hannu a wannan Lahadi kan yarjejeniyar kafin bude taron shugabannin. A yanzu dai daga cikin kasashen nahiyar 55, kasashen Benin da Eritriya ne kadai ke zama saniyar ware na kin shiga a cikin wannan wagegeyar kasuwa wacce ta kunshi mutane miliyan dubu da 200.

Ko baya ga yarjejeniyar kasuwancin, shugabannin kasashen na Afirka za su tattauna batutuwan da suka shafi 'yan gudun hijira da kuma musamman batun matsalolin tsaro masu nasaba da ayyukan kungiyoyin masu da'awar jihadi da ke kara addabar wasu kasashen nahiyar.