1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar da Benin za su hada karfi a kan makamashi

Salissou Boukari M. Ahiwa
April 27, 2023

Wata tawaga ce daga kasar Benin ta yi wata ganawa da hukumomin Jamhuriyar Nijar a kokarin da kasashen biyu ke yi na inganta huldar da ke tsakaninsu a fannoni da dabam-dabam.

https://p.dw.com/p/4QdYj
Hoto: Getty Images/AFP/J. Lhuillery

An yi wannan zaman tattaunawa ne tsakanin tawagar ministocin kasar Benin da ke karkashin jagorancin ministan kasa Abdoulaye Bio Tchane tare da takwarorinsu na Jamhuriyar Nijar a karkashin jagorancin Firaminista Ouhoumoudou Mahamadou domin dasa dan ba a kan yarjeniyoyin da kasashen biyu suka rattaba wa hannu kan harkokin tattalin arziki da cinikayya da kuma tsaro tun lokacin da shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya kai ziyara Benin a watan da ya shude.

Hakan kuma na a matsayin fada da cikawa musamman idan aka yi la’akari da kyakkyawan fatan da kasashen biyu suke da shi dangane da bututun mai da ake kokarin ganin ya isa tashar ruwan Cotonou daga kasar Nijar.

Ita ma dai daga nata bangare tawagar ta kasar Benin ta ce ta zo ne domin na farko jaddada aniyar shugaban kasar Benin, Patrice Talon, kan aniyarsa ta aiki hannu da hannu da hukumomin kasar Nijar domin karfafa hulda ta yadda kowane bangare zai gani a kasa cikin mutunci da kiyaye hakkoki na makwabtaka

Da alama dai a wannan karon bangarorin biyu na Nijar da kasar Benin za su bai wa marada kunya a fannin inganta huldar da ke tsakanin kasashen biyu, ko ma da yake matsalolin da ‘yan Nijar din ke fuskanta, sun ta’allaka ne a kan hanya ko kuma a can tashar ruwan na Cotonou da ake fatan lamarin zai sauya a nan gaba, kuma ya inganta ya zuwa kyaukyawar fuska.