1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar da Gini na yunkurin inganta harkokin tsaro da kasuwanci a tsakaninsu

Abdoulaye Mamane AmadouMay 18, 2015

A wani mataki na kara hulda da dangantaka tsakanin kasashen Nijar da Equatorial Gini shugaban kasar ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Nijar

https://p.dw.com/p/1FRWg
Niger Mahamadou Issoufou Präsidentschaftswahlen
Hoto: picture alliance/Photoshot

Hukumomin kasashen biyu dai sun tattauna a kan al'amurra da dama da suka shafi kasashen biyu musamman ma batun kasuwanci ta hanyar saka hannun jarin ‘yan Nijar a kasar Gini, ko kuma gayyato ‘yan kasar ta Gini a jamhuriyar Nijar domin shigowa kasar da hannayen jarinsu saboda bunkasar kasashen. Ko baya ga batun kasuwanci shuwagabannin biyu sun tattauna a kan batun tsaro da ke addabar yankin sahel musamman ma kasar ta Nijar dake fafutukar yaki da ta'addanci.


Ziyarar Mista Obiang Mbasogo a Nijar na zuwa ne shekaru da dama bayan rattaba hannun da kasashen suka yi da niyyar kafa wani kwamitin da zai kyautata huldodin kasashen biyu a cikin watan Janairun shekara ta 2006 a birnin Malabon kasar da kuma shuwagabanni na wancan lokacin suka amince da shi, matakin da shugaban kasa Isufu yace yana shirye a yau domin kakkabewa takardun kura

'"Nijar na shirye domin inganta duk wata hulda da kasar Gini saboda gaba dayanmu a cikin wani yanayi na aminci da yarda muka kai ga kafa yarjejeniyoyi a fannonin da suka cancanta, sune na samarda wasu hanyoyi da zasu kyautata rayukan al'ummomin kasashenmu biyu, kana ina son in yi amfani da wannan damar ta ziyararka domin sake farfado da fasahohin da muka kuduri anniyar kafawa wadanda muka daukarwa juna alkawaali tun da jimawa" Wadannan kalaman shugaban kasa ke nan Mouhamadou Issoufou.

Äquatorialguinea Präsident Teodoro Obiang Nguema neu
shugaba Teodoro Obiang Nguema ya ce aiki tare na da mahimmancin gaskeHoto: AP

Shugabannin biyu za su tinkari matsalar tsaro

Sai dai ziyarar na zuwa ne a yayinda kasashen sahel ke fama da matsalolin ta'addanci, da ke neman cin karfinsu daga ciki har da jamhuriyar Nijar inda matsalar Boko Haram da barazanar AQMI ko MUJAO ke neman toshe mashedarta zuwa ga walwala da bunkasuwarta a fannoni daban-daban. Ga dai karin bayanin shugaba Obiang Ngeuma:

"Yana da kyau mu hada gwiwa domin inganta fannin tsaronmu da samarda dabaru na bai daya saboda yin fito na fito da ta'addanci da safarar bil adama da makamai da sauran wasu miyagun dabi'u da ke bannata kimar kasashen mu".

Ko baya ba batun tsaro kasashen sun tattauna a kan huldar kasuwanci inda tawagar ta shugaban Gini ke tafe da wasu yan kasuwa da zasu gana da takwarorinsu na Nijar domin sabonta dangantakar kasuwancinsu"

Shugaban zai kammala ziyarar a yau tare da saka hannu a kan yarjejeniyoyi daban daban da suka shafi bunkasar tattalin arzikin kasashen.