1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hama Amadou zai yi takara a Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
September 22, 2020

Madugun 'yan adawar Jamhuriyar Nijar Malam Hama Amadou wanda jam'iyyarsa ta tsayar da shi takarar shugabancin kasar, ya ce ya amsa tayin kuma zai tsaya takarar ko ta halin kaka.

https://p.dw.com/p/3ir4Q
Hama Amadou
Jagoran adawar Jamhuriyar Nijar, Hama AmadouHoto: DW/S. Boukari

Babban jagoran adawar na Jamhuriyar Nijar, Malam Hama Amadou ya bayyana wannan matsaya tasa ne yayin wani taron manema labarai a Yamai babban birnin kasar. Batun makomar takarar Hama Amadou a gaban kotun tsarin mulki shi ne batun da ya kasance a sahun gaban tattaunawar tasa da 'yan jarida. A baya dai kotun ta taba yanke masa hukuncin zaman kaso na tsawon shekara guda.

Karin Bayani: Za a ci gaba da tsare Hama Amadou a gidan kaso

Dangane da wannan batu dai Malam Hama Amadou ya ce babu wani hukuncin alkali da ya hana shi 'yancinsa na yin zabe ko a zabe shi, inda ya yi kira ga magoya bayansa da su kwantar da hankulansu domin a cewarsa babu abin da zai hana shi tsayawa takara, yana mai cewa: "Gwamnati ce ke son yi wa doka karan tsaye kawai domin hana ni tsayawa takara, kamar yadda a zaben 2016 ta nemi hana ni gudanar da yakin neman zabe ba tare da yin nasara ba. A dangane da haka yanzu ba maganar doka ba ce, magana ce ta amfani da karfin iko da gwamnati ke son yi kawai. Dan haka ina kara jaddadawa cewa, ni dan takara ne a zaben da ke tafe, kuma ya zama dole ga gwamnati da wadanda ke da nauyin kula da kiyaye doka, su mutunta dokoki." 
To sai dai da aka tambaya shi cewa idan duk da hujjojin da ya gabatar na kare takararsa a gaban kotun tsarin mulki, kotun ta yi watsi da takararsa daga karshe wani mataki zai iya dauka? Hama Amadou ya amsa da cewa abin da ya wakana a kasar Mali shi ne zai wakana a Nijar: "Ina nufin irin kokowar da kawancen kungiyoyin M5 mai adawa da mulkin shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya yi. Domin a bayyana take idan har al'umma ba ta amince da wani abu ba a kasa, tana iya kawo sauyi. Idan al'umma ta sa kanta tana da karfin tilasta wa kotun tsarin mulki janye wani hukunci ko matakin da ta dauka. Dan haka ina kira ga al'umma wannan aiki nata ne. Kuma kar wani ya yi tunanin ina magana ne kan shigowar sojoji. Duk wanda ke da irin wannan tunani kan abin da na fada, to ya fitar da shi daga cikin kansa."

Hama Amadou, Parlamentspräsident in Niger
Hama Amadou ya kasance tsohon shugaban majalisar dokokin NijarHoto: DW/M. Kanta

Karin Bayani: Fargabar yin magudi a babban zabe

Ya kuma ce jita-jitar da ake yadawa ta yiwuwar kawancen adawa ya tsayar da dan takara daya a zaben shugaban kasa, abu ne da ba zai amince ba, amma dai sun sha alwashin kamawa kowanne ne zai zo zagaye na biyu daga cikin kawancen adawar na CAP 20-21. Kazalika da yake tsokaci dangane da yadda adawa ke ci gaba da bijirewa hukumar zabe da kundin zabe wanda ya sa wasu ke ganin haka zai iya janyo jinkirta zaben da tsawaita wa'adin shugaban kasa, ya ce koma wadannen irin kura-kurai ke tattare da tsarin tafiyar da zaben, ba za su taba amincewa a kara wa'adin shugaban kasa ko dage zaben daidai da minti daya.