1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin jam'iyyar Lumana ta Nijar

Salissou Boukari LMJ
February 13, 2020

A Jamhuriyar Nijar Sabon rikici ya kunno kai a babbar jam'iyyar adawa ta Lumana, bayan da ofishin ministan cikin gida ya soke manyan tarukan da bangarorin jam'iyyar ta Lumana biyu suka shirya yi a Dosso da Yamai.

https://p.dw.com/p/3XkQ1
Niger Sitz der Fraktion der Oppositionspartei Moden Fa Lumana
Jam'iyyar adawa ta Lumana a Jamhuriyar Nijar na fama da rikicin cikin gidaHoto: DW/D. Köpp

Ofishin ministan cikin gidan na Nijar wanda shi ne ke kula da jam'iyyun siyasa a kasar, ya nunar da cewa har yanzu Oumarou Noma ya sani a matsayin shugaban riko na jam'iyyar ta Lumana kaman yadda wata kotu a Yamai ta tabbatar da hakan tun farkon rikicin. Cece-kucen dai ya kunno kai ne tun daga ranar Talatar wannan makon, inda ofishin ministan cikin gida ya bai wa bangaran Noma Oumarou amsa dangane da neman izini da ya yi na kiran wani sabon taro na congres wanda ya ce za a yi shi a birnin Dosso a ranar 23 ga wannan wata na Fabarairu.

Wasikar ta Ofishin ministan cikin gidan kasar ta Nijar din ta tabbatar da cewa Oumarou Noma ne shugaban riko kuma shi ne ke da hurumin kiran babban taron na congres. Sai dai ga dukkan alamu a wannan karon, bangarorin jam'iyyar ta Lumana biyu za su bai wa marada kunya domin su zamana tsintsiya madaurinki daya. Wannan takaddama dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara aikin rijistar masu zabe a shirye-shiryen da ake na fuskantar zabuka a Jamhuriyar ta Nijar. A hannu guda kuma, a Alhamis din nan ne alkali wata kotu a Filingué ya sa hannu kan wata takadda da ta bai wa jagoran 'yan adawar ta Lumana a Jamhuriyar Nijar, Hama Amadou izinin zuwa binciken lafiyarsa a can birnin Paris na kasar Faransa, da sharadin zai dawo cikin kwanaki 15.