1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta Cimma wasu daga cikin muradun ƙarni

December 3, 2013

Shugaban ƙasar Mahamadou Issoufou shi ne ya bayyana haka a lokacin wani taron bita na ƙasashen Ƙungiyar Tarrayar Turai da na Afirka a birnin Brussels na Belgium.

https://p.dw.com/p/1ASF4
Hoto: Seyllou/AFP/Getty Images

Mahamadou Issoufu ya bayyana cewar gwamnatinsa ta cimma nasarorin aiwatar da wasu muhimman aiyyuka a fafutukar da ake yi na cimma muradun ƙarni wato MDG a shekarun 2015. Taron wanda a wannan jikon aka yi wa taken kyakyawar rayuwa ga kowa kafin nan da shekaru 2030. Shi ne karo na takwas da ake yi, wanda kuma ya tattara shugabannin na Ƙungiyar Tarrayar Turai da na ƙasashen Afirka inda suka canza yawu domin yin bita kan irin muhimman aiyyukan da aka ƙaddamar kawo yanzu, a daidai lokacin da ya rage shekaru biyu a kai shekara ta 2015 da MDD ta ware na cimma muradun ƙarni.

Nijar ta rage yawan mace-mace na mata da yara ƙanana

Muradun na ƙarni dai sun haɗa da yaƙi da talauci da yuwan da samar da ilimi da daidaito tsakanin al'umma da yaƙi da ciwon Sida da rage mutuwar yara ƙanana da mata masu juna biyu da dai sauransu. A cikin wata hira da wakiliyar DW da ke a birnin Brussels Katia Bitsch ta yi da shugaban ƙasar na Nijar wato Mahamadou Issoufou, ya shaida cewar Nijar ta yi ƙoƙarin rage yawan mace-mace na yara 'yan ƙasa da sekaru biyar da ake samu da talauci da kuma yuwan, sai dai ya ce da sauran aiki.

Europäische Entwicklungstage Barroso und Sierleaf 26.11.2013
Mahammadou Issofou a tsakiyar shugabannin Afirka da na Turai a taron na BrusselsHoto: picture-alliance/dpa

Ya ce : ''A kwai wasu muradun guda shida da suka yi saura ,kuma ya rage mana shekaru biyu yanzu kafin shekarun 2015 mai yiyuwa a gaza cimma wasu manufofin, kafin lokacin shi ya sa muke nan muna tattaunawa domin yin tunani a kan abin da ya zama wajibi a yi. Ba maganar a rage talauci ba muke a kai,manufofin da muke son a cimma shi ne na kauda talauci kwata-kwata. Ba za a yi cimma wannan manufofi ko ba,sai an samar da hanyoyin kauda banbanci da ke tsakanin al'umma. Tare da samar da hanyoyin ingata rayuwar masu ɗan ƙarfi da kuma kula da wani sabon ƙalubalen shi ne maganar tsaro saboda a lokacin da aka ɓulo da muradun ƙarnin ba a yi tunanin wannan matsala ba ta tsaro.''

Sai an tashi tsaye domin tabbatar da lamarin tsaro a yankin Sahel

Batun na tsaro na daga cikin batutuwan da shugaban na Nijar ya ambato a wajen taron masammun ma dangane da irin halin da yanki ya samu kansa a ci wanda aka tambaye shi ko yana da fargaban lamarin na rasin tsaro ya bazu zuwa ƙasarsa. Ya ce : '' Haƙiƙa Nijar na kewaye da ƙasashen da ke fuskantar barazana misali Mali da Libiya da Najeriya, sai dai har kawo yanzu mun ɗauki matakai na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasarmu wacce ke zaman misali na gari na kwanciyar hankali a cikin yankin Sahel inda har yanzu tsugune ba ta ƙare ba.'' Shugaban na Nijar ya ba da misali da shirinsa ga taron wato shirin nan, na ɗan Nijar ya ciyar da ɗan Nijar wanda ake kira da sunan 3N. Wanda ya ce ya yi tasiri so sai wajen canza alƙalluma a fannin samar da cimmaka ga al'umma. Inda a shekarun 2008 kishi 26 cikin ɗari na 'yan Nijar ɗin ke fama da yuwan yayin da a shekarun 2012 ake da kishi 12 cikin ɗari.

Nigerianische Truppen bereiten sich auf Einsatz in Mali vor
Sojojin Nijar a MaliHoto: Reuters

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu