1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Cin hanci na dakile ci-gaba a Nijar

Salissou Boukari LMJ
September 20, 2019

Wani rahoto da Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF ya fitar, ya bayyana yadda matsalar cin hanci da ta yi katutu a Jamhuriyar Nijar ke haddasa babban koma baya ga kokarin da hukumomi ke yi na samar da ci-gaba.

https://p.dw.com/p/3Pxwn
Niger Anti-Korruptionsinitiativen
Yaki da cin hanci da rashawa na tafiyar hawainiya a Nijar

Rahoton na Asusun ba da Lamuni na Duniyar IMF, ya ce a 'yan shekarun baya-bayan nan kasar ta Nijar ta kyautata yanayinta na mulki tare da karfafa matakai na yaki da cin hanci da karbar rashawa, domin kuwa gwamnati ta dauki matakai masu kayatarwa da za su bayar da dama a yaki duk wani cin hanci. Sai dai kuma rahoton ya ce duk da wannan aniya da hukumomin na Nijar suka dauka, akwai manyan kura-kurai da ke hana ruwa gudu, domin kuwa binciken da aka yi ya nunar cewa cin hanci ya watsu a sassa daban-daban na fadin kasar har ma ya samu gindin zama, kana akwai karancin bin dokoki na tafiyar da harkokin mulki a bangaran ma'aikatun gwamnati, wanda hakan ke zama cikas ga bunkasar bangaren ma'aikatu masu zaman kansu, musamman ma kanana.

Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Mahamadou Issoufou
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou IssoufouHoto: AFP/I Sanogo

Sanin kowa ne dai hukumomin na Nijar na cewa suna nuna jajircewarsu wajen yaki da cin hanci da rashawa, inda ma suka dauki matakai da ka iya bayar da damar yin hakan kamar rattaba hannu a yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da cin hanci da rashawa da yarjejeniyoyi irin na kungiyar Tarayyar Afirka da ma na kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS, baya ga hukumar kasa mai kula da yaki da cin hanci da rashawa ta HALCIA wadda ma a shekara ta 2016 aka kara mata karfi domin ta yaki cin hanci a kasar ta Nijar. Akwai kuma tsari na masu bincike a cikin ma'aikatu na gwamnati da kuma kotun ma'aikata, rahoton ya gano cewa kasar na yin sako-sako wajen aiwatar da yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, kuma duk da cewa hukumar yaki da cin hanci ta kasa HACIA na da 'yanci. Sai dai har yanzu hukumar na karkashin fadar shugaban kasa, sannan tana fuskantar tarin matsaloli na kudin da zai ba ta damar tafiyar da ayyukanta yadda ta kamata. DW dai ta yi kokarin jin ta bakin gwamnati ta hanyar aikewa da sako ga ministan da ke magana da yawun gwamnatin ta Nijar kan wannan rahoto, sai dai hakanta bai cimma ruwa ba. Amma kuma masu lura da al'amura a Jamhuriyar ta Nijar na ganin cewa duk da wadannan dokoki, sai fa an soma nuna misali daga koli, ta yadda za a soma bai wa gawa kashi domin mai rai ya ji tsoro.