1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu

Binta Aliyu Zurmi
December 27, 2020

Alumma a Jamhuriyar Nijar na fita zuwa rumfunan zabe domin kada kuri'u. Wannan zaben dai shi ne irinsa na farko da zababben shugaban kasar farar hula zai mika mulki ga wata gwamnatin farar hula. 

https://p.dw.com/p/3nFQ9
Niger Wahllokal in Niamey
Hoto: Reuters/J. Penney

Sama da mutane miliyan bakwai ne suka yi rijistar zabe a kasar. 'Yan takarar shugabancin kasar 30 ne ke kokarin karbar mulki daga hannun shugaba mai barin gado Muhammadou Issoufou wanda ya zamo shugaban kasa a shekarar 2011, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2010.

Ana ganin koma wa ye ya yi nasarar lashe zaben na yau zai fuskanci manyan kalubale da suka hada da matsalar tsaro da na cin hanci da rashawa. Can a dayan hannun kuwa a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, su ma a yau ne a su ke gudanar da manyan zabuka na shugaban kasa da na 'yan majalisu duk kuwa da matsalar tsaron da kasar ke fuskanta a halin da ake ciki.

Za a fafata zaben na yau ne tsakanin shugaba Faustin-Archange Touadera da wasu mutum  17. Ofishin kare hakkin bil'adama na MDD duniya ya yi gargadin hare-haren kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai ka iya kawo cikas a zabukan da ma rayukan alumma fararen hula.

Ko a Jumma'ar da ta gabata jami'an wanzan da zaman lafiya na majalisa mutum uku ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da wata kungiya ta kai. A cewar MDD 'yan tawayen na samun goyon bayan tsohon shugaban kasar ne Francois Bozize