1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Zanga-zanga kan kasafin kudin 2018

Ramatu Garba Baba
December 21, 2017

A Yamai jama’a da dama sun rufe shaguna don kauracewa sana’oi bayan kira da kungiyoyin fararen hula suka yi don adawa da dokar tsarin kasafin kudi da gwamnati ta yi wanda kuma tuni majalisar kasar ta amince da ita.

https://p.dw.com/p/2pnEG
Niger - Demonstration gegen den Terror in Zinder
Hoto: DW/L. Hami

Tun da safiya masu zanga-zangar suka fito dauke da alluna dauke da rubuce-rubuce na nuna adawa da matakin gwamnatin tare da yin kira da ta gaggauta sauya matakin na ta kan dokar kasafin kudin shekara mai zuwa, lamarin da ya sa jama’a da dama suka kauracewa wuraren sana’oinsu wasu na fargabar barkewar rikici wasu kuma sun bi umarnin ne don nuna goyon baya ga kungiyoyin.

Kungiyoyin fararen hula da suka hada zanga-zangar a jahar Damagaram kuwa sun yi tattaki ya zuwa fadar gwamnantin inda suka mika takardar kokensu da a ciki suka bukaci gwamnati da ta sauya mataki kan kasafin kudin. Masu zanga-zangar sun kamalla tattakin cikin lumana ba tare da hatsaniya ba kamar yadda aka taba yi a can baya, lamarin da a wancan lokacin ya kai ga raunata tarin jama’a da kuma janyo asarar dukiya.Yanzu dai kungiyoyin sun tsayar da ranar Asabar don sake gudanar da wata sabuwar zanga-zangar.