1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nuna rashin amincewa da sabuwar dokar Masar

November 25, 2013

Shugaban Masar ya amince da dokar da ta takaita taron mutane a cikin kasar.

https://p.dw.com/p/1ANQ2
Hoto: G.Guercia/AFP/GettyImages

Shugaban gwamnatin wucin gadin kasar Masar Adly Mansour ya amince da ayar da ake takaddama wadda ta hamramta taruwar mutane fiye da 10 ba tare da amincewar gwamnatin ba. Duk wanda ya karya dokar zai fuskanci tara mai tsanani da dauri a gidan fursuna.

Sabuwar dokar ta tanadi sanar da hukumomi shirin gudanar da zanga-zanga kwanaki uku kafin lokacin.

Sabuwar dokar ta kasar Masar ta wuce wadda tsohon Shugaba Hosni Mubarak ya yi amfani da ita tsanani, lokacin da yake rike da madafun ikon kasar. A farkon watan Yuli sojoji suka kifar da gwamnatin Mohamed Mursi, kuma tun wannan lokaci kasar ta fada cikin sabon rikicin siyasa. Kungiyoyin kare hakkin dan Adama na kasar sun soki matakin gwamnatin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh