1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya ce dole a daƙile kisan gilla

December 17, 2012

Shugaban Amirka Barack Obama ya sha alwashin amfani da duk ƙarfin da yake da shi, wajen kare sake faruwar kisan gilla.

https://p.dw.com/p/173cz
Hoto: picture-alliance/dpa

Shugaban Amirka Barack Obama ya sha alwashin amfani da duk ƙarfin da yake da shi, wajen kare sake faruwar kisan gilla irin wanda aka yi wa yara 'yan makaranta 20 da malamai shida a Newtown da ke jihar Connecticut.

Obama ya gana da al'umar Newtown wajen da aka samu faruwar lamarin, kuma ya nuna kaɗuwa da kisan na mutane 26. Dan bindigan ya hallaka mahaifiyarsa, da mutanen 26 kuma daga bisani ya hallaka kansa.

Shugaba Obama ya nemi hadin kan Amirka wajen dakile wannan matsala, inda ake samun masu harbin kan mai-uwa da wabi, saboda yadda makamai ke hannun mutane.

Sannan ya tabbatar wa iyalan mutanen da abun ya shafa cewa, sauran Amirkawa na tare da su.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal