1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya fara ziyara a nahiyar Turai

March 24, 2014

Shugaban Amirka Barack Obama da sauran takwarorinsa na G7 za su hallarci wani taro na makamashin nukiliya da za a gudanar a birnin The Hague na kasar Holland.

https://p.dw.com/p/1BUhK
Obama Rede zur Ukraine 17.03.2014
Shugaban Amirka Barack ObamaHoto: Reuters

Obaman har wa yau zai tattauna da shugabannin kasashen Turai dangane da rikicin da ke wakana tsakinin Ukraine da Rasha musamman ma ballewar yankin nan na Kirimiya wanda yanzu haka ya hade da Rasha.

Baya ga ziyarar da zai yi a Turai, shugaban na Amirka zai kuma ziyarci Saudi Arabiya inda zai tattauna da Sarki Abdallah, kuma ana sa ran tattaunawar shugabannin biyu wadda za a yi ta birnin Riyadh za ta maida hankali ne kan halin da ake ciki a Siriya da ma dai shirin nukiliyar Iran wanda ke cigaba da jawo daga hakarkari tsakanin Iran din da kasashen yamma.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe