1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya kammala rangadin nahiyar Afirka

July 5, 2013

Haduwa tsakanin shugaban na Amirka da magabacinsa George W Bush a birnin Dar es Salaam ta kasance kololuwar ranar karshe ta ziyararsa a nahiyar.

https://p.dw.com/p/192gj
U.S. President Barack Obama and former President George W. Bush (R) attend a memorial for the victims of the 1998 U.S. Embassy bombing in Dar es Salaam July 2, 2013. REUTERS/Jason Reed (TANZANIA - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Bari mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda ta mayar da hankalin kan rangadin kasashen Afirka guda uku da shugaban Amirka Barack Obama ya kammala a ranar Talata.

"Ziyarar da ya kai kasar Tanzaniya ta kawo karshen rangadin mako guda da Shugaba Obama ya kai nahiyar Afirka. Wata haduwa tsakanin Obama da magabacinsa tsohon shugaban Amirka George W Bush ta kasance kololuwar ranar karshe ta ziyararsa a birnin Dar es Salaam. Bush da Obama sun ajiye furanni a dandalin dogon yaro na tunawa da mutanen da harin ta'addancin da aka kai kan ofishin jakadancin Amirka Dar es Salaam a shekarar 1998. Obama wanda ya ziyararci kasashen Senegal da Afirka ta Kudu da kuma Tanzaniya ya dauki hankali sosai musamman game da kalaman da ya yi nahiyar. A Senegal ya yi magana game da 'yancin 'yan luwadi a matsayin wani hakki na dan Adam bisa la'akari da al'adun mai yi masa nasauki. A Afirka ta Kudu shugaban na Amirka ya yi tir da cin hanci da rigingimun siyasa a Afirka sannan ya yi alkawarin taimakawa a fannin samar da hasken wutar lantarki a nahiyar Afirka."

Mandla bai gaji halin kakansa ba

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a babban labarinta mai taken Mandla Mandela cewa ta yi jikan Nelson Mandela bai dauki kyakkyawan halin kakansa ba, sannan sai ta ci gaba kamar haka.

REFILE -ADDING RELATIONSHIP OF MBUSO TO MANDLA Mandla Mandela (C), grandson of former South African president Nelson Mandela, talks to his lawyer at the start of a news conference in Mvezo, in the Eastern Cape of South Africa, July 4, 2013, a day after a court order to return the bodies of three of Mandela's children to Qunu was carried out. Two years ago, Mandla exhumed the bodies from Qunu, where Mandela grew up, and moved them to Mvezo, where Mandla has built a visitor centre and a memorial centre dedicated to his grandfather. Last week, a rival faction of the family, led by Mandla's aunt Makaziwe and including Mbuso, brother of Mandla, won a court order for the bodies to be returned to Qunu - an edict carried out late on Wednesday after a last-minute legal bid by Mandla failed. REUTERS/Siegfried Modola (SOUTH AFRICA - Tags: POLITICS)
Shari'a kan Mandla MandelaHoto: Reuters

"Ana iya cewa mutum kamar Nelson Mandela ya cancanci samun kyakkyawar makoma, amma bisa ga dukkan alamu hakan na dushewa a kullu yaumin. Yanzu dai ya fito fili cewa biyu daga cikin 'ya'yansa mata sun yi kokarin karkata wani asusun ajiya na Mandela don amfanin kansu. Sannan yanzu kuma da tsohon dan gwagwarmayar neman 'yanci mai shekaru 94 ke kwance a asibiti rai kwakwai mutu kwakwai, iyalansa na takaddama game da wurin da za a binne shi idan ta Allah ta zo. Jigo a wannan takaddama shi ne jikan Mandela wato Mandla mai shekaru 39, wanda kuma a lokaci guda yake zama magajinsa a fagen siyasa. Sai dai Mandla masanin kimiyyar siyasa, ya fi ya yi gadon kudi maimakon siyasa daga kakan nasa. A bara ya sayar da lasinsin watsa shirye-shiryen bikin jana'izar Nelson Mandela a kan kudi Euro dubu 300. Sannan yanzu wasu daga cikin 'yan uwansa 16 sun kai kararshi biyo bayan sake binne 'ya'yan Mandela a Qunu, wurin da Mandela din ya taso. Sai dai ya lashe amansa a yanzu bisa umarnin kotu."

ARCHIV - Der schwerer Menschenrechtsvergehen beschuldigte Ex-Präsident des Tschad, Hissane Habre (Archivfoto vom 18.01.1987), soll im Senegal vor Gericht gestellt werden. Das kündigte Senegals Präsident Abdoulaye Wade am Sonntag (02.07.2006) beim Gipfeltreffen der Afrikanischen Union in Gambias Hauptstadt Banjul an. Senegal hatte sich lange dagegen gesperrt, Habre vor Gericht zu stellen. Der Ex-Diktator lebt dort seit seinem Sturz vor 15 Jahren im Exil. +++(c) dpa - +++
Tsohon shugaban kasar Chadi Hissene HabreHoto: picture-alliance/dpa

Tsohon dan mulkin danniya ya shiga hannu

Tsohon madugun 'yan tawaye kuma tsohon shugaban Chadi ya shiga hannu, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai cewa shekaru 22 tsohon dan mulkin kama karya Hisseni Habre ya yi ta cin karensa babu babbaka a Senegal sai dai yanzu zai gurfana gaban kotu. Jaridar ta ce ana zargin Habre wanda yayi mulki daga 1982 zuwa 1990 da kisan abokan adawa fiye da 1200. A wasu rahotannin ma yawansu ya kusan dubu 40. Za a dai dauki wasu watanni kafin a fara yi wa tsohon shugaban na Chadi shari'a, watakila ma za a kai shekara ta 2015 domin ba a sani ba ko a Senegal za a yi zaman sauraron shari'ar ko kuma tasa keyarsa za a yi zuwa kotun duniya dake binin The Hague.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu