1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya yaba rawar da Mandela ya taka

June 29, 2013

Halin da tsohon shugaban ke ciki ya mamaye ziyarar aiki da shugaban na Amirka ke yi a Afirka ta Kudu, kasar da Mandela ya zama bakar fatan farko da ya shugabanceta.

https://p.dw.com/p/18yVl
Hoto: Reuters

Shugaba Barack Obama na Amirka ya yaba irin rawar da tshohon shugaban Afirka ta Kudu Nelson Mandela ya taka wajen karfafa wa mutane da dama guywa a duniya. A lokacin wani taron manaimana labarai na hadin guwa da ya gudanar da abokin aikinsa na Afirka ta Kudu Jacob Zuma, Obama ya ce yaki da wariyar launin fata da Mandela ya yi wani babban abin alfahari ne a gareshi.

Fadar mulki ta White House ta riga ta bayyana cewa shugaban na Amirka bai zai je asibinti domin duba lafiyar Nelson Mandela da ke ckin wani mummunan hali ba. Amma kuma ta nunar da cewar zai gana da iyalan Mandela mai shekaru 94 da haihuwa.

A ranar Lahadi idan Allah ya kai mu Barack Obama zai ziyarci tsibirin Roben, inda bakar fatan farko da ya shugabaci Afirka ta Kudu ya shafe shekaru 18 daga cikin shekaru 27 da ya kasance a tsare. Afirka ta Kudu dai na zama zango na biyu na ziyarar aiki da Obama ke yi a nahiyar Afirka, wacce zai kammala da Tanzaniya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal