1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shirya bikin tuna ranar haihuwar Mandela

Ramatu Garba Baba
July 16, 2018

Tsohon shugaban kasar Amirka Barack Obama na daga cikin wadanda za su gabatar da kasidu a taron da za a soma gobe Talata a gabanin bikin tunawa da ranar haihuwar Nelson Mandela a Afirka ta Kudu.

https://p.dw.com/p/31XPZ
Afrika - US Präsident Obama besucht Nigeria, Uganda und Kenia in 2013
Hoto: Getty Images/C. Somodevilla

 

Mandela wanda ya yi gwagwarmayar 'yantar da Afirka ta Kudu daga mulkin wariyar launin fata dama samar da daidaito a kasar, ya kasance abin koyi a tsakanin al'ummar yankin Afirka.Tuni mahukuntan kasar suka kammala shirye-shiryen karrama marigayin, a ranar 18 ga watan Yuli da Mandela zai cika shekaru 100.

Obama, da yanzu haka ke ziyara a Kenya, kasarsa ta asali,  zai ja hankulan matasa, kan sanin mahinmancin 'yanci dan adama da alfanun daidaito a tsakanin al'umma.  An tsara mahinman batutuwa a bikin da zummar zaburar da matasa a yunkurin da a ke na ciyar da nahiyar gaba.