1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obasanjo ya fice daga jam'iyyar PDP

Ubale Musa/ASFebruary 16, 2015

Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

https://p.dw.com/p/1EcU7
Porträt - Olusegun Obasanjo
Hoto: Getty Images

Shugaba Obasanjo ya bayyana hakan ne a wani taro dazu inda ya umarci shugaban mazabarsa na PDP da ya yaga katinsa na zama dan jam'iyyar ta PDP. Jim kadan bayan ficewarsa, tsohon shugaban na Najeriya kana tsohon shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar ta PDP ya ce ya gwammace ya kasance uban kasa maimakon cigaba da zama a PDP din.

Nigerianischer Präsident Goodluck Jonathan 11.11.2014
Hoto: picture-alliance/AP

Gabannin ficewarsa daga PDP din dai, Obasanjo ya yi ta samun takun saka da shugaban kasar Goodluck Jonathan da jiga-jigan jam'iyyar PDP musamman ma dai na kudu maso yammacin kasar inda nan jiharsa ta Ogun ta ke. Ficewar ta Obasanjo daga PDP din dai na zuwa ne gabannin zaben shugaban kasar da za a gudanar a karshen watan gobe.

Tuni dai shugaban kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP din Cif Tony Anenih ya sanar da cewar ba su girgiza da ficewar Cif Obasanjo din daga jam'iyyar ba, hasali ma inji shi ba za su yi kewarsa ba ko alama. Wadannan kalamai na Cif Anenih dai na zuwa ne bayan da reshen PDP na jihar Ogun ya ce ya sallami Obasanjo sa'o'i biyun bayan da ya ce ya raba gari da jam'iyyar.

Shi kuwa Dr. Umar Ardo guda daga cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP din cewa ya yi "ficewar tsohon shugaban wata babbar asara ce duba da irin muhimmancin da ya ke da shi a jam'iyyar" yayin da 'yan adawa a kasar irinsu Buba Galadima na cewar su kam kamar su zuba ruwa a kasa su sha don farin ciki.

Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

A daura da wannan masana harkokin siyasa a kasar na cewar ficewar Obasanjo daga PDP din ka iya kasancewa wani babban hadari ga uwar jam'iyyar duba da yiwuwar da ake da ita na ya yaki jam'iyyar musamman a zabukan da ke gaba, inda a hannu guda 'yan kasar ke cigaba da maida martani mabanbanta game da wannan batu.