1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ostareliya ta tsaurara doka kan gudun hijira

December 5, 2014

Majalisar dokokin kasar Ostareliya ta amince da wata doka mai karin tsanani kan 'yan gudun hijira, a wani mataki na karya lagon masu kwarara zuwa kasar ta hanyoyin ruwa

https://p.dw.com/p/1DzYJ
Hoto: picture-alliance/dpa

Bayan dai da aka tafka mahawara tsakanin 'yan majalisun a ranar Alhamis (04.12.2014) majalisar ta aminta da kwaskwarimar da aka yi wa dokar kan 'yan gudun hijira a wannan kasa, inda a nan gaba za a bayar da takardar visa ce ga wadanda aka tabbatar cewa 'yan gudun hijira ne shi ma ta tsawon shekaru uku kawai ba tare da an ba su izin zama na dindindin ba. Inda a tsawon shekarun nan uku za a binciki halin da kasashen da suka fito ke ciki, domin ganin ko za su ci gaba da zama a matsayin masu gudun hijira, ko kuma a mayar da su.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo